Kafofin watsa labaran Isra'ila sun rawaito cewa an kashe shugaban ofishin siyasa na Hamas Yahya Sinwar a Gaza.
Biyu daga cikin gidajen yaɗa labarai na Isra'ila, KAN da N12 News sun ambato jami'an Isra'ila a ranar Alhamis suna cewa Sinwar ya mutu.
Babu wani tabbaci a hukumance daga Hamas.
Da farko dai rundunar sojin Isra'ila ta ce tana duba yiwuwar kashe Sinwar bayan wani farmaki da ta kai a Gaza kan mayakan gwagwarmayar Falasdinawa uku.
An nada Sinwar a matsayin shugaban Hamas bayan kashe tsohon shugaban siyasa na ƙungiyar Ismail Haniyeh a Tehran na Iran a watan Yuli.
Sinwar shi ne shugaban Hamas da Isra'ila ta fi nema ruwa a jallo, inda Tel Aviv ta zarge shi da kitsa harin kan iyaka da ƙungiyar ta kai a ranar 7 ga Oktoban bara, wanda ya sa Isra'ila ta ƙaddamar da wani mummunan yakin soji a Gaza wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 45,000 a cewar sanarwar hukumomin lafiya na yankin.
Watanni goma da yakin Isra'ila, yankunan Gaza da dama sun zama kango a a loakcin da aka hana shiga da abinci da ruwan sha da magunguna.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce babu alamun akwai wadanda aka yi garkuwa da su a ginin da aka kashe mutanen uku.