1704 GMT — Jiragen yaƙin Isra'ila sun bugi Asibitin Ƙawancen Turkiyya da Falasɗinu a Gaza
Jiragen yaƙin Isra'ila sun bugi Asibitin Ƙawancen Turkiyya da Falasɗinu a Gaza, lamarin da ya jawo mummunar ɓarna, kamar yadda daraktan asibitin ya ce.
"Jiragen yaƙin Isra'ila sun tarwatsa hawa na uku na Asibitin Ƙawancen Turkiyya da Falasɗinu, wanda shi ne kaɗai asibitin da ke kula da masu cutar kansa a Gaza,: kamar yadda Dr Subhi Skaik ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Ya ƙara da cewa harin da Isra'ilan ta kai ya jawo "mummunar ɓarna sakamakon tashin da wuta ta yi kafin daga bisani a kashe ta."
Skaik ya kuma ce lamarin ya lalata wasu daga cikin na'urorin aiki da kuma sanya rayuwar ma'aikata da marasa lafiya cikin hadari.
A wata sanarwa da aka fitar tun da fari, ya ce rundunar sojin Isra'ila tana ci gaba da kai hare-hare kan asibitoci a cikin kwanakin nan.
1334 GMT — ‘Yan Isra’ilan de ka tsare a hannun Hamas sun nemiNetanyahu ya saki fursunonin Falasɗinu
“Ku ceto mu yanzu ku kuma saki dukkan mutanensu,” in ji wata ƴar Isra’ila da take tsare a Gaza, yana mai kira ga Firaminista Benjamin Netanyahu a wani bidiyo da ƙungiyar Hamas ta saki, kan batun fursunonin Falasdinu da ke gidajen yarin Isra’ila.
Hamas ta saki wani bidiyo da ta ce ya nuna wasu mata uku daga cikin aƙalla mutum 239 da Isra’ila ta ce an sace su zuwa Gaza a lokacin da ƙungiyar ta kai hare-hare ranar 7 ga watan Oktoba.
“Muna cikin wannan halin ne saboda gazawarka (Netanyahu) kan abin da ka jawo ranar 7 ga watan Oktoba, ya zama dole a kanka ka sake mu duka,” a cewar ɗaya daga cikin waɗanda ake tsare da su din.
Ba za a iya tabbatar da ko su waye matan ba a cikin bidiyon mai tsawon sakan 76, inda ɗaya daga cikinsu take kira ga Isra’ila da ta ƙulla yarjejeniyar sakin dukkan mutanen da ake tsare da su.
1108 GMT — Afirka ta Kudu ta yi kira ga dakarun MDD su kare fararen hula a Gaza
Afirka ta Kudu ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta aika dakarun wanzar da zaman lafiya don zu kare fararen hula a yankin Gaza na Falasdinu da aka yi wa ƙawanya daga hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa a kan ƙungiyar Hamas.
Afirka ta Kudu ta daɗe tana ƙoƙarin ganin an samu zaman lafiya a yankin, inda take kamanta lamarin Falasɗinawa da irin nata na fafutukar samun ƴanci daga mulki mallakar da aka yi mata da ya kawo ƙarshe a shekarar 1994.
Da take yin kira kan aika dakarun wanzar da zaman lafiya, Afirka ta Kudu ta kuma ci gaba da nuna goyon bayanta ga Falasɗinawa fiye da sauran ƙasashe, inda waɗansu suka yi kira da a tsagaita wuta ko kuma a ba da damar shigar da kayan agaji Gaza.
0805 GMT — Dakarun Isra'ila sun katse babbar hanyar da ta hada arewaci da kudancin Gaza
Dakarun Isra'ila sun shiga yankin Zaytun na Gaza ta kasa, inda suka katse babbar hanyar da ta hada arewaci da kudancin yankin, kamar yadda ganau suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
"Sun katse hanyar Salahedin kuma sun bude wuta kan duk wani abin hawa da ke kan hanyar," in ji wani mazaunin yankin.
A gefe guda, tankokin yakin Isra'ila sun matsa daga gabashin Gaza inda suka isa Hanyar Salah al Din da ke Birnin Gaza, a cewar ganau da suka yi hira da kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Kakakin rundunar sojin Isra'ila Daniel Hagari ya shaida wa manema labarai cewa suna "nausawa a hankali" zuwa cikin Gaza kuma za su kara kai hare-hare "daki-daki, kamar yadda bukatar yakin take."
0855 GMT — ‘Yan Isra’ila sama da 1,538 aka kashe zuwa yanzu
Sama da ‘yan Isra’ila 1,538 aka kashe tun bayan da aka soma yaki tsakanin Isra’ila da Falasdinawa a ranar 7 ga watan Oktoba, kamar yadda kafar watsa labarai ta Isra’ila KAN ta ruwaito.
KAN ta bayyana cewa akwai gawarwaki 823 da aka gano zuwa yanzu inda tuni aka binne sama da 715.
Tun a jiya Lahadi, mai magana da yawun sojin Isra’ila Daniel Hagari ya bayyana cewa sojojinsu da suka rasa rayukansu a Gaza sun kai 311.
0800 GMT — ICC ta gargadi Isra'ila kan jinkiri wurin shigar da kayan agaji Gaza
Babban mai shigar da kara na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya a ranar Lahadi ya yi gargadi kan cewa hana shigar da kayayyakin agaji cikin Gaza zai iya zama laifi.
Karim Khan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai wata ziyara a mashigar Rafah, inda ya bayyana cewa akwai manyan motoci dauke da kayayyakin agaji wadanda ake bukatarsu da suka makale aka ki barin su shiga Gaza.
Mista Khan ya jaddada cewa akwai bukatar wadannan kayayyakin su kai ga mabukata a cikin gaggawa.
0720 GMT — Masar na shirin yadda motoci dauke da kayan agaji za su shiga Gaza
Masar na gudanar da shirye-shirye domin manyan motoci 60 da ke dauke da kayan agaji su shiga Zirin Gaza a ranar Litinin ta iyakar Rafah, kamar yadda kafafen watsa labarai na kasar ruwaito.
Kungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent a wata sanarwa ta daban da ta fitar ta bayyana cewa akwai manyan motoci 118 da suka shiga Falasdinu ta iyakar kasar daga kudu tun bayan da Isra’ila ta soma kai mata hare-hare a wannan watan.
Sai dai a cewarta, ba a bari an shigar da man fetur ba. Haka kuma tuni kungiyoyin agaji ke korafi kan karancin fetur da magunguna da ake fama da su a zirin Gaza da Isra'ila ta yi wa kawanya.
0000 GMT — Dole Isra’ila ta kare fararen-hula a Gaza, a cewar Fadar White House
Fadar White House ta Amurka ta ce dole ne Isra’ila ta kare al’ummar Gaza da ba su ji ba ba su gani ba ta hanyar iya bambance ‘yan kungiyar Hamas da kuma fararen-hula, a yayin da shugabannin duniya ke ci gaba da kiraye-kiraye a gaggauta kai kayan agaji yankin na Falasdinu da yaki ya daidaita.
Isra’ila ta zafafa kai hare-harenta ta sama da ta kasa bayan wani harin ban mamaki da kungiyar Faasdinwa ta Hamas ta kai mata mako uku da suka wuce, wanda hukumomin Isra’ila suka cewa ya yi sanadin kashe akalla mutum 1,400.
Tun bayan 7 ga watan Oktoba, an kashe Falasdinawa 8,000 a hare-haren da Isra’ila ta yi ta kai wa, wadanda rabinsu yara ne, in ji ma’aikatar lafiya ta Gaza.
Tun da fari Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa fararen-hula sun fara take doka a Gaza bayan da dubban mutane suka fasa rumbun adana abinci na MDD din inda suka kwashe alkama da filawa da sauran kayayyaki.
Zubar da jinin da ake yi ya sa gwamnatin Biden ta yi gargadin cewa dole ne Isra’ila ta bai wa fararen hula kariya.
0004 GMT — An lalata masallatai 47 da coci 3 a Gaza tun daga 7 ga Oktoba
Masallatai 47 da kuma coci uku ne suka lalace sakamakon hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa Gaza, kamar yadda ofishin watsa labarai na gwamnati a yankin ya fada.
“Hare-haren Isra’ila a Gaza sun jawo lalacewar masallatai 47 da coci uku da kamarantu 203 da kuma gine-ginen gwamnati 80,” a cewar daraktan ofishin, Salama Maarouf a wani taron manema labarai.
Ya ce yawan ma’aikatan lafiyan da Isra’ila ta kasha kuwa sun kai 116 da mambobin tawagogin agaji da kuma ‘yan jarida 35.