Jam'iyyar Leba ta Birtaniya za ta ɗare karagar mulki bayan lashe babban zaɓen kasar inda ta samu kujeru 326 da za su ba ta damar kafa gwamnati a majalisar dokoki.
"Nauyi irin wannan na zuwa da aiki da dama," in ji shugaban na Leba Keir Starmer yayin da yake ganawa da magoya bayansa a wajen gangamin murnar samun nasara a Landan a ranar Juma'a, jim kaɗan bayan sanar da sakamakon da ya nuna ya yi nasara.
Tsohon shugaban jam'iyyar Leba a Birtaniya Jeremy Corbyn da jam'iyyar ta dakatar saboda kalaman nuna ƙyama ga Yahudawa, ya sake lashe zaɓe zuwa majalisa a matsayin ɗan takara mai zaman kansa.
Corbyn, mai shekara 75, wanda ya wakilci mazaɓar Islington North da ke Landan sama da shekara 40, ya lashe kujerar a karon farko ba tare da jingina ga Leba ba.
Ya jagoranci babbar Jam'iyyar Leba ta adawa wadda ta kama hanyar dawowa kan mulki bayan zaɓen ranar Alhamis, amma ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar bayan mummunan kayen da ya sha a 2019.
Farage da Galloway
Nigel Farage, shugaban jam'iyyar Sauyi ta Birtaniya ya lashe kujera ɗaya tilo a majalisar dokokin Birtaniya a karon farko a garin Clacton-on-Sea da ke gaɓar tekun Ingila, a yayin da masu zaɓe suka ƙaurace wa jam'iyyar Ra'ayin Riƙau ta Firaminista Rishi Sunak.
Farage da ra'ayinsa na nuna ƙyama ga 'yan gudun hijira, goyon bayan Brexit ya sanya shi zama ɗaya daga cikin sanannun 'yan siyasar Birtaniya kuma masu kawo rarrabuwar kai, cikin sauƙi ya kayar da ɗan takarar Jam'iyyar Ra'ayin Rikau Giles Watling wanda a baya ya lashe kujerar.
Shiga zaɓe da ya yi cikin ban mamaki a watan da ya gabata, bayan a baya ya yanke ba zai shiga ba, ya habaka goyon bayan jam'iyyar Sauyi ta UK a fadin kasar.
Sanannen dan siyasa George Galloway ya sha kaye a babban zaben na Birtaniya, inda dan takarar Leba a garin Rochdale na arewacin Ingila ya yi nasara.
Galloway ya zauna a majalisa tsawon watanni hudu kacal bayan lashe zaben cike-gurbi da mutuwar tsohon dan majalisa mai wakiltar yankin ta sanya aka shirya shi.
A baya a watan Maris, gangamin Galloway na goyon bayan Falasdinawa ya sanya shi samun kuri'u daga jama'ar Musulmin garin.