1720 GMT — Isra'ila za ta gane kurenta na kashe Janar din rundunar juyin juya hali na Iran
Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya lashi takobin cewa tabbas Isra'ila za ta gane kuranta na kashe Sayyed Razi Moussavi babban kwamandan dakarun kare juyin juya hali na Iran a Syria.
"Ba tare da ko shakka ba, wannan mataki wata alama ce ta takaici da gazawar gwamnatin Isra'ila ta mamaya a yankin," in ji Raisi a cikin wata sanarwa da ta ƙara da cewa Isra'ila "tabbas za ta gane kurenta a wannan laifin".
1500 GMT — Jiragen ruwan Japan sun guje wa bin Bahar Maliya suna bi ta Afirka ta Kudu
Jiragen ruwa na dakon kaya na Japan suna sauya hanya don guje wa bi ta Bahar Maliya saboda fargabar yiwuwar kai hari, a yayin da ake nuna damuwa kan jinkirin da ake samu na jigilar kayayyaki.
Kamfanonin jigilar kayayyaki na Japan Nippon Yusen da Mitsui O.S.K. sun sauya akalar jiragensu daga bin Bahar Maliya saboda hare-haren da aka kai kan jiragen ruwa na baya-bayan nan.
Wani kamfani Kawasaki Kisen Kaisha shi ma yana yin irin wannan sauye-sauye.
An dauki matakan wucin gadi na wucewa daga da kuma zuwa Turai, kamar yadda gidan rediyon Japan NHK ya rawaito a ranar Litinin.
1438 GMT — Za a daɗe ana yaƙin Gaza, ba za a gama nan kusa ba: Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce yaƙin da ake gwabzawa a Gaza bai kai ga kawo ƙarshe ba, ya kuma yi watsi da abin da ya kira a matsayin raɗe-raɗin ƙarya da kafafen yada labarai ke yadawa cewa gwamnatinsa na iya dakatar da yaƙi da Hamas.
“Ba za mu tsaya ba, muna ci gaba da fafatawa, kuma za mu ƙara tsananta fadan a cikin kwanaki masu zuwa, kuma za a dauki tsawon lokaci ana gwabzawa, kuma ba a kusa aamawa ba,” kamar yadda ya shaida wa ‘yan majalisar daga jam’iyyarsa ta Likud, a cewar wani dan majalisar a wata sanarwa.
1414 GMT — Karancin kayan kula da lafiya a Gaza ya laƙume rayukan dubban Falasdinawa
Akalla mutum 9,000 ne suka mutu a Gaza sakamakon rashin kayayyakin aikin asibiti a yayin da Isra'ila ke kai wa hari, kamar yadda ofishin yada labaran gwamnati ya bayyana.
1348 GMT — Mutum 250 aka kashe a Gaza cikin awa 24 — Ma'aikatar Lafiya
Akalla Falasdinawa 250 ne suka mutu yayin da wasu 500 suka jikkata sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu ya kai 20,674 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta yi wa ƙawanya.
Ma'aikatar ta kuma ƙara da cewa mutane 54,536 ne suka samu raunuka tun bayan fara yakin Isra'ila a yankin.
1415 GMT — Hamas na zargin Isra'ila da huce fushin rasa sojojinsu kan fararen hulan Gaza
Kungiyar Hamas ta zargi Isra’ila da aikata ta’addanci kan farar hula a Gaza domin huce fushin rasa sojojinsu.
Zargin na zuwa ne jim kadan bayan an kashe akalla Falasdinawa 70 a hari ta sama a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Maghazi a tsakiyar Gaza, kamar yadda hukumomin lafiya suka bayyana.
“A duk lokacin da ‘yan gwagwarmaya suka yi galaba kan sojojin Nazi, suna aikata ta’addanci kan farar hula wadanda ba za su iya kare kansu ba tare da da taimakon [Shugaban Amurka Joe Biden],” in ji babban mamba a kungiyar Hamas Izzat al Rishq a wata sanarwa.
1200 GMT — Fafaroma ya bukaci a taimaka wa jama'ar Gaza a sakonsa na Kirsimeti
Fafaroma Francis a ranar Litinin ya bukaci a yi gaggawar kai agajin jin kai a Gaza da kuma tsagaita wuta.
Fafaroman ya bayyana hakan a sakonsa na Kirisimeti inda ya kuma bukaci a saki fursunonin yakin da ake tsare da su.
Zuciyata tana bakin ciki ga wadanda suka mutu a mummunan harin ranar 7 ga Oktoba, kuma ina sake jaddada kiran gaggawa na a sako wadanda ake garkuwa da su,” in ji fafaroman mai shekara 86.
0828 GMT — Isra'ila ta ce an kara kashe wasu sojojinta a Gaza
Rundunar sojin Isra’ila a ranar Litinin ta sanar da cewa an kashe karin sojojinta biyu a yayin arangama da mayakan Falasdinu a Zirin Gaza, wanda hakan ya kawo adadin sojojin da aka kashe tun daga 7 ga watan Oktoba zuwa 489.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce an kashe Netai Maisels mai shekara 30 da Rani Tameer mai shekara 20 wadanda ke yaki a arewacin Falasdinu.
0000 GMT — Isra'ila ta kashe mutum 78 a hare-haren da ta kai Gaza a jajibirin Kirsimeti
Jami'an lafiya na Falasdinu sun ce wasu hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a jajibirin Kirsimeti sun yi sanadin mutuwar mutum akalla 78.
Isra'ila ta kaddamar da hare-haren ne da tsakar daren Litinin inda ta wayi garin yau tana luguden wuta musamman a yankin Al Bureij da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda ganau da kafafen watsa labarai na Falasdinu suka tabbatar.
An kashe akalla mutum 70 a hari ta sama da jiragen yakin Isra'ila suka kai yankin Maghazi da ke tsakiyar Gaza, a cewar mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar Falasdinu Ashraf Al Qidra, yana mai cewa galibinsu mata ne da kananan yara.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana nazari kan abin da ya faru a Maghazi kuma tana so ta rage yawan fararen-hular da ke cutuwa. Kungiyar Hamas ta musanta zargin da Isra'ila ke yi mata cewa tana buya a wuraren da ke da dandazon jama'a inda take yin amfani da mutanen a matsayin garkuwa.
Kungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent ta wallafa bidiyoyin mutanen da suka jiakkata a yayin da ake tafiya da su asibiti. Ta ce jiragen yakin Isra'ila sun yi ta luguden wuta a manyan hanyoyin da ke tsakiyar Gaza, inda suka hana motocin daukar marasa lafiya wucewa.
0219 GMT — 'Zuciyoyinmu suna Bethlehem' : Fafaroma Francis
Fafaroma Francis ya yi kira a zauna lafiya yayin da ya jagoranci addu'o'in Jajibirin Kirsimeti a Majami'ar St. Peter’s Basilica da ke Vatican a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da yin luguden wuta a Gaza.
"A daren nan, zuciyoyinmu suna Bethlehem, inda aka sake yin watsi da Yariman Zaman Lafiya saboda yaki,” in ji Fafaroma a jawabinsa ga kusan mutum 6,500, yana tunawa ne da Yesu Almasihu.