sra'ila ta kashe mutum 3,117 a Lebanon / Hoto: AA

Juma'a 8 ga watan Nuwamban 2024

1624 GMT — Hare-haren Isra'ila a Lebanon sun hallaka aƙalla mutum 3,117, tare da jikkata mutum 13,888 tun watan Oktoban 2023, a cewar Ma'aikatar lafiya ta Duniya.

1622 GMT - Sojojin Isra'ila sun ce sun tare ƙarin rokoki da jirage marasa matuka da aka harba daga Lebanon

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta tare ƙarin rokoki da jiragen yaki da aka harba daga kasar Lebanon zuwa yankunan arewaci da tsakiyar Isra'ila.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce bayan kunnuwar jiniya ta sama mai ankararwa a yankuna da dama a arewaci da kuma tsakiya, wasu rokoki guda biyar sun keta sararin samaniyar Isra'ila.

Ya kara da cewa kariyar da ake da ita ta sama ta katse yawancin rokokin.

1250 GMT — Yawan mutanen da hare-haren Isra'ila suka kashe a Gaza sun kai 43,508

Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza da aka yi wa kawanya ta ce akalla mutum 43,508 ne suka mutu a cikin sama da watanni 13 na yakin da Isra'ila ta yi kan ɗan ƙaramin yankin.

Adadin wadanda suka mutu ya hada da mutum 39 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, a cewar ma'aikatar, wadda ta ce mutane 102,684 ne suka jikkata a Gaza tun lokacin da aka fara yakin a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Ƙarin labarai 👇

0116 GMT — Lebanon ta ce abin da Isra'ila ke yi na far wa dakarun MDD 'laifukan yaƙi ne'

Lebanon ta yi tur da harin jirgi marar matuƙi da Isra'ila ta kai birnin Sidon da ke kudancin ƙasar wanda ya kashe farar hula uku da kuma jikkata sojojin Lebanon da na Majalisar Dinkin Duniya da dama, tana mai ayyana hakan a matsayin "laifin yaƙi".

Dakarun wanzar da zaman lafiya biyar sun jikkata a harin, wanda aka kai kusa da birnin Sidon na kudancin Lebanon, in ji MDD.

Rundunar sojin Lebanon ta tabbatar da cewa an kai harin ne da wani jirgin Israi'la marar matuƙi a kan wata mota, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum uku da ke ciki tare da jkkata uku daga sojojinta a wani shingen bincike da ke kusa da wajen.

Ministan Harkokin Wajen Lebanon ya ce ƙasar ta yi kakkausan Allah wadai da cin zalin na Isra'ila tare da yin kira ga ƙasashen duniya da su yi tur da irin wadannan hare-hare a kuma ɗora wa Isra'ila alhakin hakan.

Ma'aikatar ta bayyana harin a matsayin "zafafa wa kan abin da Isra'ila ke yi na far wa dakarun wanzar da zaman lafiya na UNIFIL, da sojojin Isra'ila da fararen hula, kuma laifukan yaƙi ne da take dokokin jinƙai na ƙasashen duniya."

TRT World