Wani hoto da Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta fitar ya nuna ministan kasar yana musabaha da takwaransa na Saudiyya da kuma takwaransu na China bayan kammala taron/Hoto AFP

Manyan jami'an diflomasiyyar Saudiyya da Iran sun gana a China, ganawa ta farko a hukumance tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen a cikin fiye da shekara bakwai, kamar yadda kafar watsa labarai ta CCTV ta ruwaito.

Gidan talabijin na Saudiyya Al-Ekhbariya, ya nuna Yarima Faisal bin Farhan Al Saud da takwaransa na Iran Hossein Amirabdollahian, suna musabaha kuma sun zauna dab da juna, a yayin ganawar da aka yi ranar Alhamis a Beijing, babban birnin China.

Gidan talabijin na kasar Iran ya ce ministocin biyu sun gana ne don tattaunawa kan batun bude ofisoshin jakadancinsu.

A wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka saki bayan taron, Faisal bin Farhan da Amirabdollahian sun ce yarjejeniyar kyautata alakarsu za ta taimaka wajen "kawo tsaro da zaman lafiya" a yankin Gabas ta Tsakiya.

"Bangarorin biyu sun jaddada muhimmancin ganin an wanzar da yarjejeniyar ta Beijing, da ganin an yi aiki da ita ta hanyar da za a fadada amincewa da juna da hadin kai da taimaka wa wajen samar da tsaro da zaman lafiya da ci gaba a yankin."

Taron na ranar Alhamis na zuwa ne wata guda bayan da kasashen biyu suka amince su farfado da dangantakar diflomasiyyarsu da kuma sake bude ofisoshin jakadancinsu a watan Mayu.

Sannan an yi taron ne a lokacin da jami'an diflomasiyyar suke ta kokarin kawo karshen yakin Yemen da aka shafe tsawon lokaci ana yi, wani rikici da Saudiyya da Iran ke da hannu dumu-dumu a ciki.

Wannan ganawa ita ce ta farko da manyan jami'an diflomasiyya daga kasashen biyu suka yi tun shekarar 2016, a lokacin da Saudiyya ta yanke alaka da Iran sakamakon kutsen da masu zanga-zanga suka yi cikin ofishin diflomasiyyar Saudiyya a Iran din.

Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa ne kan wani fitaccen malamin Shia tare da wasu mutum 46, lamarin da ya jawo mummunar zanga-zangar, inda har aka kutsa ofishin jakadancinta a washegari.

A baya-bayan nan ne Shugaba Xi Jinping na China ya taimaka wajen cimma yarjejeniya mai ban mamaki tsakanin Iran da Saudiyya, manyan abokan hamayyar juna a Gabas ta Tsakiya, don kyautata dangantakar diflomasiyyarsu.

Hakan dai ya zama wani lamari da ke nuna yadda tasirin China ke karuwa a yankin Gabas ta Tsakiya wanda Amurka take sanya wa ido matuka.

Bayan daukar dogon lokaci ana zaman doya da manjan da ya rura wutar rikice-rikice a Gabas ta Tsakiya, Saudiyya da Iran sun amince da kawo karshen matsalar tare da sake bude ofisoshin jakadancinsu bayan gagarumin shiga tsakanin da China ta yi a watan da ya gabata.

Rawar da Beijin ta taka cikin sirri na sasanta Tehran da Riyadh ya jijjiga al'amura a Gabas ta Tsakiya, yankin da Amurka ta shafe gwamman shekaru tana shiga tsakani kan al'amuransa, inda take fada a ji kan harkokin tsaro da na diflomasiyya.

Tsawon shekaru ana kai ruwa rana

Dangantakar Tehran da Riyadh ta yi muni tun shekarar 2015, bayan da Saudiyya da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa suka shiga cikin yakin Yemen, inda mayakan Houthi masu kawance da Iran suka hambarar da gwamnatin kasar wacce Saudiyya ke goyon baya tare da kwace iko da babban birnin kasar Sanaa.

Wannan yarjejeniya dai, ga Saudiyya aba ce da za ta kyautata tsaro. Kasar ta zargi Iran da bai wa mayakan Houthi makamai wadanda suke kai wa biranen Saudiyya hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka.

A shekarar 2019, Riyadh kai tsaye ta dora alhakin wani mummunan hari da aka kai kan kamfanin mai na Aramco a kan Iran, lamarin da ya jawo tsaiko ga samar da fetur dinta.

Tehran ta yi watsi da zarge-zargen.

TRT World