Alkaluma daga Ma'aikatar Cikin Gida ta Falasdinu sun nuna cewa kawo yanzu Isra'ila ta kashe fiye da mutum 11,000./Hoto:Reuters

Dubun dubatar mutane ne a fadin duniya suka gudanar da jerin zanga-zanga ranar Asabar domin yin kira ga Isra'ila ta kawo karshen kisan kare-dangi da take yi wa Falasdinawa a Gaza.

Alkaluma daga Ma'aikatar Cikin Gida ta Falasdinu sun nuna cewa kawo yanzu Isra'ila ta kashe fiye da mutum 11,000 — yawancinsu mata da kananan yara da tsofaffi — sannan ta jikkata dubbai, kana an raba mutum fiye da miliyan daya da muhallansu.

An gudanar da zanga-zanga a Afirka da Latin Amurka da Turai da Gabas ta Tsakiya inda masu gangamin suke ci gaba da Allah wadai da Isra'ila kan hare-haren da take kai wa Gaza.

REUTERS

Masu gangami sun rike kwalaye da ke Allah wadai da Isra'ila a yayin da mambobin kungiyar kare hakkin dan'adam da na Musulmai suka yi jerin gwano don nuna goyon baya ga Falasdinawa a birnin Buenos Aires na kasar Argentina.

SABC

Dubban mutane ne suka yi zanga-zanga a birnin Cape Town domin nuna goyon baya ga Falasdinawa tare da yin tir da Isra'ila kan hare-hare babu kakkautawa da take ci gaba da kaiwa a Gaza.

Masu zanga-zangar sun hada da 'yan kungiyoyin kare hakkin bil'adama da kungiyoyin addinai, ciki har da Musulmai da Kiristoci da Yahudawa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Anadolu da ke Turkiyya ya rawaito.

REUTERS

Masu gangami sun rike wata katuwar tutar Falasdinu domin nuna goyon baya ga Falasdinawa a birnin Barcelona na kasar Sifaniya.

AFP

Masu zanga-zanga a Place de la Nation a birnin Paris na Faransa sun rika daga tutocin Falasdinu a yayin da suke kira a tsagaita wuta a hare-haren da Isra'ila ke kai wa a Gaza.

AFP

A Place de la Republique da ke birnin Brussels na kasar Belgium, dubun dubatar mutane ne suka fantsama kan tituna domin nuna goyon baya ga Falasdinawa da yin Allah wadarai da Isra'ila kan kashe-kashe da take yi a Gaza.

AFP

Masu zanga-zanga a tsakiyar Landan rike da kwalaye a yayin da suka tsaya a kusa da wani wuri na wucin-gadi na tunana da Falasdinawa da Isra'ila ta kashe a Gaza.

AFP

Masu fafutuka a Isra'ila sun yi zanga-zanga a kusa da Ma'aikatar Tsaron Kasar da ke birnin Tel Aviv, Israel, inda suka yi kira a tsagaita wuta.

AFP

Masu zanga-zanga suna daga tutocin Falasdinawa sanna suna yin kira da a yi wa Falasdinawa adalci a gangamin da suka yi a Tunis, babban birnin Tunisia.

TRT Afrika da abokan hulda