Sojojin Isra'ila sun rutsa fafaren hula a arewacin Gaza: MDD / Hoto: Reuters

Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024

1613 GMT Wani hari ta sama da Isra'ila ta kai ya kashe Falasdinawa akalla takwas tare da raunata wasu da dama a unguwar Sheikh Radwan da ke birnin Gaza, kamar yadda ma'aikatan lafiya suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

1421 GMT — Sojojin Isra'ila sun rutsa fafaren hula a arewacin Gaza: MDD

Ofishin kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya kaɗu matuƙa kan yadda Isra'ila take kai mummunan hare-hare a arewacin Gaza sama da mako guda, inda ta ce dubun dubatan fararen hula ne suka maƙale ba tare da abinci ko kayan abinci ba.

"A karkashin inuwar tashe-tashen hankula a Gabas ta Tsakiya, ga dukkan alamu sojojin Isra'ila sun katse Arewacin Gaza gaba daya daga sauran yankunan Zirin Gaza tare da gudanar da yaki ba tare da la'akari da 'yancin rayuwa da tsaron Falasdinawa fararen hula ba," ofishin ya ce.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, ta samu rahoton cewa sojojin Isra'ila sun tara tuddan yashi a wani muhimmin wuri, inda suka yi nasarar dakile arewacin Gaza tare da yin luguden wuta kan masu yunkurin guduwa.

0322 GMT — Isra'ila ta ƙona Falasɗinawa 4 da ransu a harin da ta kai tantunan 'yan gudun hijira

Isra'ila ta ƙona Falasɗinawa aƙalla huɗu da ransu, tare da jikkata mutum fiye da 40 a wani hari da ta kai a tantunan da fararen-hula da ta kora daga gidajensu suke samun mafaka a Gaza, a cewar kafofi watsa labaran yankin.

Gobara ta tashi a tantunan da ke jikin Asibitin al-Aqsa Martyrs, wanda ke birnin Deir al Balah, sakamakon harin, a cewar kamfanin dillanacin labaran FalasɗinuWAFA.

Hotuna da bidiyoyin da aka riƙa watsawa a shafukan intanet sun nuna yadda mutane suka makale a cikin tantunan sannan hayaƙi ya turnuƙe su.

2316 GMT —Adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin da Isra'ila ta kai a wata makaranta a Gaza ya ƙaru zuwa 22

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon wani hari ta sama da Isra'ila ta kai a wata makaranta a tsakiyar Gaza ya ƙaru zuwa 22, a cewar ofishin watsa labarai na gwamnatin yankin.

Ya ƙara da cewar sojojin Isra'ila "suna sane cewa dubban mata da yara da aka kora daga gidajensu suna samun mafaka a makarantar ta Mufti amma suka kai mata hari da bama-bamai."

Falasɗinawa suna yin sallar jana'iza ga wasu 'yan'uwansu da aka kai Asibitin Nasser bayan kisan da Isra'ila ta yi musu a harin da ta kai birnin Rafah / Hoto: AA

Ƙarin bayani 👇

0212 GMT — Amurka ta nemi Isra'ila a bi hanyar diflomasiyya kan yaƙin Lebanon

Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin ya ce akwai buƙtatar Isra'ila ta daina amfani da ƙarfin soji kana ta rungumi hanyar diflomasiyya a yaƙin da take yi a Lebanon.

Da yake magana ta wayar tarho da Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant, Austin ya ce ya ika ta'aziyyarsa bisa mutuwar sojojin Isra'ila a wani hari na jirgi mara matuƙi da Hezbollah ta kai musu.

"Na jaddada buƙatar tabbatar da tsaron lafiyar (Dakarun Wanzar da Tsaro na MDD a Lebanon) UNIFIL da Sojojin Lebanon da kuma buƙatar mayar da hankali kan sulhu ta hanyar diflomasiyya da daina amfani da ƙarfin soji," in ji shi a saƙn da ya wallafa a shafin X.

2142 GMT — Isra'ila ta ce harin da Hezbollah ta kai da jirgi mara matuƙi ya kashe sojojinta 4

Rundunar sojojin Isra'ila ta ce sojojinta huɗu sun mutu sakamakon harin da Hezbollah ta kai da jirgi mara matuƙi a sansaninsu da ke kudancin Haifa.

"An kashe sojoji huɗu na IDF a harin, sannan guda bakwai sun yi mummunar jikkata,"a cewar wata sanarwa da rundunar sojojin ta fitar.

TRT World