Babu tabbaci kan abin da ya jawo gobarar, sai dai gobarar ta yi ɓarna a ginin gidan tarihin. / Hoto: Others

1432 GMT — Gobara ta tashi a gidan ajiye kayan tarihi na Isra'ila

Gobara ta tashi a gidan ajiye kayan tarihi na Isra’ila da ke Birnin Ƙudus a ranar Lahadi, kamar yadda kafafen watsa labaran Isra’ilar suka ruwaito.

Gobarar ta fara ne a wani daji kusa da ginin inda ta kai ga gidan tarihin, sai dai masu kashe gobara sun yi ƙoƙari domin kashe wutar, kamar yadda kafar watsa labarai ta portal Walla ta Isra’ila ta ruwaito.

Zuwa yanzu babu tabbaci kan abin da ya jawo gobarar, sai dai wutar ta yi ɓarna a ginin wanda shi ne gidan tarihi mafi girma na Isra'ila da ke ɗauke da muhimman kayayyakin tarihi.

0832 GMT — Mayaƙan Hezbollah sun kai hari wani barikin sojin Isra'ila

Mayaƙan Hezbollah na Lebanon a ranar Lahadi sun ce sun kai hari kan wani barikin sojojin Isra’ila a Tuddan Golan na Syria da Isra’ila ta mamaye.

A wata sanarwa da mayaƙan suka fitar, sun ce sun yi amfani da jirage marasa matuƙa domin kai harin a barikin Yarden wanda ke kan iyakar Lebanon.

Hakazalika mayaƙan sun ce sun kai hari kan na’urar Iron Dome wadda Isra’ilar ke amfani da ita domin daƙile hare-hare musamman na makamai masu linzami.

Ana ta samun rikici a kan iyakar Lebanon da Isra'ila, inda aka yi ta musayar wuta tsakanin sojojin Isra'ila da Hezbollah, wanda shi ne fada mafi muni tun bayan da bangarorin biyu suka gwabza kazamin yaƙi a shekara ta 2006.

2211 GMT — Masu shiga tsakani na Qatar da Masar da Amurka sun yi kira ga Isra'ila da Hamas su "ƙarƙare" cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Shugaban Amurka Joe Biden ya tsara, a daidai lokacin da dakaraun Isra'ila ke ƙara zafafa ruwan wuta a kudancin Gaza.

To sai dai Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu tuni ya jaddada cewa ƙasarsa za ta ci gaba da yaƙi har sai yaƙin ya cimma manufarsa.

Ya nanata wannan matsayi ne a ranar Asabar, yana mai cewa "sharuɗan da Isra'ila ta gindaya don kawo ƙarshen yaƙin ba su sauya ba: rusa Hamas ta fuskar soja da shugabanci, da kuɓutar da duka mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma tabbatar da cewa Gaza ba za ta sake zama barazana ga Isra'ila ba".

Ita kuma ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa ta ce tana duban shirin na Isra'ila da Biden ya tsara da "kyakkyawan fata."

A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa, Qatar da Amurka da Masar sun ce " a msatayinmu na masu shiga tsakani a tattaunawar da ake ci gaba da yi don tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da waɗanda ake tsare da su", sun yi "kira ga Hamas da Isra'ila su yi aiki da yarjejeniyar da daftarin Shugaban Joe Biden ta tsara".

2241 GMT — Dubban Isra’ilawa sun nemi a yi musayar fursunoni da ƙungiyoyin Falasaɗinawa

Dubban Isra’ilawa sun yi zanga-zanga a Tel Aviv don neman a cimma yarjejeniyar musayar fursunoni da ƙungiyoyin Falasaɗinawa, sannan a gudanar da zaɓe da wuri, a cewar kafofin watsa labarai.

Dubban ɗaruruwan mutanen ne suka shiga zanga-zangar a baban birnin ƙasar da ake yi duk mako a Dandalin Kaplan a tsakiyar Tel Aviv, suna neman a cimma yarjejenyar musayar fursunoni nan take, abin da zai kai ga sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza, kamar yadda jaridar Yedioth Ahronoth ta rawaito.

Iyalen mutanen da aka yi garkuwa da su sun nemi Benjamin Netanyahu ya yi amfani da daftarin tsagaita wuta da Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar ranar Juma’a.

TRT World