Rayuwar jarirai akalla 120 da suke cikin kwalba a asibitoci a Gaza na cikin hadari bayan da man fetur ya fara karewa a yankin da aka yi wa kawanya, kamar yadda hukumar yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi.
Isra'ila ta kashe yara fiye da 1,750 kawo yanzu sanadin hare-hare ta sama da take kai wa Gaza a matsayin martani ga harin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba, kamar yadda Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Falasdinawa ta bayyana.
Asibitoci suna fuskantar matsanancin karancin magunguna da man fetur da ruwa ba kawai don kulawa da dubban mutane da suka jikkata ba hatta mutanen da ke neman kulawa ta yau da kullum a fiye da tsawon mako biyu na hare-haren da Isra'ila take kai wa a Gaza.
"Yanzu haka muna da jarirai 120 wadanda suke cikin kwalba, a cikinsu muna da guda 70 da ke kan na'urar janyo numfashi, shakka babu wannan ne babban abin damuwa," in ji mai magana sa yawun Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya Jonathan Crickx a ranar Lahadi.
Matsalar wutar lantarki tana daga cikin manyan abubuwan damuwa ga asibitocin kwararru bakwai a fadin Gaza da ke kula da jarirai bakwaini ta fuskar taimaka musu wajen numfashi da sauran kulawa, misali idan wasu sassan jikinsu ba su gama girma ba.
Karancin man fetur ya jawo cikas ga ayyukan agaji
Isra'ila ta bayar da umarnin mamaye gaba daya Gaza bayan Hamas ta kai mata hare-hare, inda kungiyar ta kashe mutum 1,400 kamar yadda mahukunta a Isra'ila suka bayyana.
Yayin da ake ci gaba da fuskantar yankewar wutar lantarki, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a ranar Alhamis ta yi gargadin cewa man fetur din injinan janareton asibitoci ya fara karewa.
Hukumar WHO ta ce kimanin mutum 1,000 da ke bukatar wankin koda za su fada hadari idan injinan janareton suka daina aiki.
Manyan motoci dauke da kayan agaji guda 20 ne suka shiga Gaza daga Masar a ranar Asabar, sai dai babu man fetur a cikin kayayyakin.
Isra'ila tana jin tsoron cewa man fetur zai iya taimaka wa Hamas, kodayake akwai ragowa a Gaza wanda ake amfani da shi a injinan janareto don na'urorin kiwon lafiya su ci gaba da aiki.
"Idan aka sa su (jarirai) a kan na'urar taimaka wa mutum numfashi, haka yana nufin, idan wuta ta yanke, dole mu damu game da rayuwarsu," in ji mai magana da yawun Hukumar UNICEF kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
A ranar Asabar Ma'aikatar Kiwon Lafiya a Gaza ta ce jarirai bakwaini 130 na hadarin mutuwa saboda karancin man fetur.
Mata kimanin 160 ne suke haihuwa a kowace rana a Gaza, kamar yadda hukumar da ke kula da yawan jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, wacce ta yi kiyasin akwai mata masu ciki 50,000 a yankin mai kunshe da mutum miliyan 2.4.
Yayin da Isra'ila take kai hari ga Hamas, wacce ta kai munanan hare-hare kan Isra'ila a tarihi tun bayan kafa ta a shekarar 1948, yara ne adadinsu ya fi yawa a cikin jumullar mutum 4,385 da aka kashe da ma'aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta ruwaito.
Gaba daya iyali, ciki har da mata masu ciki, an kashe su a hari ta sama kuma a kowace rana iyaye suna ganin ta'asar da ake yi, gawawwakin jarirai a cikin likafani a kan tituna.
Likitoci a asibitin Najjar Hospital a Rafah sun yi magana a ranar Alhamis yadda suka yi kokarin ceto wani jarirai da ke cikin mahaifiyarsa wacce aka kashe a wani hari ta sama yayin da take zaune a gida.
Sa'o'in da suka gabata, yara takwas aka kashe yayin da suke bacci a gida a garin Khan Younis a kudancin Gaza.