Litinin, 11 ga watan Nuwamban 2024
1338 GMT — Firaiministan Malaysia Anwar Ibrahim ya yi kira da a gaggauta kawo karshen kisan ƙare dangi da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a Gaza.
Da yake jawabi ga babban taron Ƙasashen Musulmi na Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmi da aka gudanar a Riyadh babban birnin kasar Saudiyya, Anwar ya bayyana cewa, "rikicin bil'adama" yana faruwa a Gaza.
Ya bukaci kasashe mambobin kungiyar OIC da kasashen duniya da su magance matsalolin da Falasdinawa ke ciki.
0925 GMT — Sojojin Isra'ila sun kasa mamayar ko da ƙauye ɗaya a Lebanon — Hezbollah
Rundunar sojin Isra'ila ta kasa mamayar ko da ƙauye ɗaya a Lebanon tun bayan da ta fara kai hare-harenta cikin ƙasar a watan Satumba, a cewar ƙungiyar Hezbollah.
"Bayan shafe kwana 45 ana mummunan yaƙi, har yanzu maƙiya sun kasa mamayar ko da ƙauye ɗaya a ƙasar Lebanon," kamar yadda mai magana da yawun ƙungiyar Hezbollah, Mohammad Afif ya shai da taron manema labarai a kudancin Beirut, inda Isra'ila ke ta kai hare-haren sama a wajen.
Ƙarin labarai 👇
0854 GMT — Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta daƙile harin jirage marasa matuƙa 4 daga Iraƙi
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta daƙile harin jirage marasa matuƙa huɗu da aka harba daga Iraƙi a yayin da ake tsaka da tashe-tashen hankulan yankin.
Wata sanarwar sojin ta ce an harba jiragen ne daga gabashin, wata kalma da rundunar sojin Isra'ila ke amfani da ita don bayyana hare-hare daga Iraƙi.
An harbo biyu daga cikin jiragen tun kafin su shiga sararin samaniyar Isra'ila, in ji rundunar sojin, ba tare da yin ƙarin bayani a kan sauran biyun ba.
0044 GMT — Kungiyar Euro-Med ta buƙaci MDD ta ayyana yunwa a arewacin Gaza
Kungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Euro-Med ta buƙaci kungiyoyin kasa da kasa da na Majalisar Dinkin Duniya da su ayyana a hukumance cewa ana fama da yunwa a arewacin Gaza, inda aka hana agaji da kayayyaki isa ga dubban mazauna yankin sama da kwanaki 50.
Bisa la'akari da cewa Isra'ila ta hana shigar da kayayyaki da kayan agaji ga dubban mazauna yankin arewacin Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya sama da kwanaki 50 a yanzu, dole ne hukumomin kasa da kasa da na Majalisar Dinkin Duniya da abin ya shafa su ayyana yunwa a yankin."
Kungiyar ta ce a cikin wata sanarwa daga hedkwatar ta Geneva. Ta ƙara da cewa, amfani da yunwa a matsayin makami daya ne daga cikin ayyukan kisan gillar da Isra'ila ke ci gaba da yi a Zirin Gaza, wanda ya hada da kashe-kashen jama'a da gudun hijira.
0058 GMT — Masar da Malaysia sun amince su yi aiki tare don cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Lebanon
Shugaban ƙasar Masar Abdel Fattah el Sisi ya sanar da cewa shi da firaministan Malaysia Anwar Ibrahim suna da aniya irin ɗaya ta yin aiki tare don cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Gaza na Falasɗinu da kuma Lebanon.
Tattaunawar da ta haɗa da batutuwan yanki da na ƙasashen duniya, inda shugabannin biyu suke jaddada buƙatar ci gaba da ƙoƙarin ganin an dakatar da rikici a Gaza da Lebanon da kuma ba da damar shigar da kayayyakin agaji cikin yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya.