Erdogan

1342 GMT — Erdogan na Turkiyya ya soki yadda Amurka ke murkushe zanga-zangar jami'o'i

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi magana a kan batun zanga-zangar da ake yi a jami'o’in Amurka, yana mai cewa hukumomi na nuna rashin tausayi na murƙushe dalibai da malamai masu goyon bayan Falasdinu.

“Dalibai da malamai waɗanda suka san ya kamata da suka haɗa har da masu adawa da aƙidar tsananin kishin Isra’ila a wasu manyan jami’o’in Amurka suna zanga-zangar nuna adawa da kisan kiyashi (a Gaza),” in ji Erdogan a wani taron da aka gudanar a Ankara.

“Ana cin zarafin wadannan mutane da wulaƙanta su da azabtar da su saboda suna cewa dole ne a daina kisan kiyashi, ya kuma kara da cewa ana “kore ma’aikatan jami’ar ne saboda suna goyon bayan Falasdinawa.

Erdogan ya ce: "Dimokuraɗiyyar Ƙasashen Turai ta ta’allaka ne wajen tabbatar da muradun Isra'ila." Duk abin da ya saɓa wa muradun Isra'ila, ya saɓa wa dimokradiyya, ƙyama a gare su."

0855 GMT — Falasɗinawa da Isra'ila ta kashe sun kusa 34,600 a yayin da ake ci gada da luguden wuta a Gaza

Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe tun da ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza sun kai 34,596 a yayin da take ci gaba da luguden wuta a yankin, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Gaza.

A wata sanarwa da ta fitar, ma'aiakatar ta ƙara da cewa mutum sama da 77,816 sun jikkata sakamakon hare-haren.

“Isra'ila ta kashe aƙalla Falasɗinawa 28 tare da jikkat 51a awanni 24 da suka gabata,” in ji sanarwar.

“Mutane da dama na binne a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine da kan hanyoyi kuma masu aikin ceto sun kasa kuɓutar da su,” a cewar sanarwar.

0320 GMT Jami'an tsaron Isra'ila da na Amurka sun tattauna kan Rafah ta wayar tarho

Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin da takwaransa na Isra'ila Yoav Gallant sun tattauna game da yiwuwar ƙaddamar da hare-hare ta ƙasa a birnin Rafah na kudancin Gaza, a cewar ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon.

A tattaunawar da suka yi ta wayar tarho, Austin da Gallant sun yi musayar yawu game da ci gaba da garkuwa da fursunoni ake yi da kuma batun kai kayan agaji, a cewar wata sanarwa da kakakin ma'aikatar Manjo Janar Pat Ryder ya fitar.

Austin ya jaddada aniyar Amurka wajen ganin an dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su tare da shigar da kayayyakin agaji Gaza da tsaron fararen-hula da ma'aikatan agaji, in ji Ryder.

An yi tattaunawar wayar tarho ɗin ne bayan Firaiminista Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ƙaddamar da hare-hare a Rafah - / Hoto: AA

2216 GMT — 'Yan jam'iyyar Democrat sun yi kira ga Biden ya hana Isra'ila mamaye Rafah

Gwamnatin Shugaba Joe Biden tana shan sabuwar suka daga 'yan jam'iyyar Democrat domin ya hana Isra'ila ƙaddamar da cikakkiyar mamaya a Rafah, birnin da kimanin rabin mutanen Gaza miliyan 2.4 suke samun mafaka.

'Yan majalisar wakilai hamshin da bakwai daga cikin 212 na jam'iyyar Democrat sun rattaba hannu kan wata wasiƙa inda suka yi kira ga gwamnatin Biden ta tsawatar da gwamnatin Firaiminista Benjamin Netanyahu mai kunnen-ƙashi daga mamayar birnin Rafah da ke kan iyakar Masar.

"Muna kira a gare ka da ka ɗauki mataki na doka nan-take don hana duk wani taimako ga gwamnatin Isra'ila, ciki har da tallafin da majalisa ta amince da shi, da zummar hana ƙaddamar da mamaya a Rafah," a cewar wasiƙar da suka rubuta ranar Laraba.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ranar Laraba ya ce har zuwa lokacin bai ga wani shirin Isra'ila na ƙaddamar da mamaya a Rafah ba, yana mai jaddada cewa mahukunta a Washington ba za su "goyi bayan" hakan ba.

Democrats urge Biden to prevent Israeli invasion of Rafah

0009 GMT — Ɗaliban Jami'ar Fordham ta New York sun kafa sansanin nuna goyon baya ga al'ummar Gaza

Wasu ɗalibai na Jami'ar Fordham da ke Birnin New York sun kafa sansani inda suke nuna goyon baya ga al'ummar Gaza, a wani mataki na bin sawun takwarorinsu a faɗin Amurka da ke kira a kawo ƙarshen hare-haren da Isra'ila take kai wa Falasɗinawa.

Ɗalibai da dama sun mamaye Cibiyar Leon Lowenstein, wani gini da ke reshen jami'ar na Lincoln Center, inda suka kafa sansani biyar a wani mataki na nuna goyon baya ga Falasɗinawa.

Mahukuntan jami'ar sun aika wa ɗaliban wasiƙa ta hannun shugabar Lincoln Center Jenifer Campbell inda suka umarce su da su fice daga Jami'ar Fordham nan-take.

Kazalika jami'ar ta ce za ta dakatar da ɗalibai daga shiga ɗakunansu da ajujuwa da rubuta jarrabawa da ma duk wasu al'amura na jami'ar.

TRT Afrika da abokan hulda