1459 GMT — Bankin Duniya ya sanar da ba da tallafin dala miliyan 20 a Gaza
Bankin Duniya ya sanar da ba da sabon tallafin dala miliyan 20 don samar da taimakon jinƙai ga al'ummar Gaza, da ya haɗa da dala miliyan 10 don sayen kayan abinci.
Sanarwar da bankin ya fitar ta ce, tallafin zai kai ga kimanin mutum 377,000, wani ɓangare ne na wani babban shirin agaji na dalar Amurka miliyan 35 ga Zirin Gaza.
Sanarwar ta ce an riga an kai dala miliyan 15 na farko na agajin gaggawa.
1226 GMT — Falasdinawa da ake tsare da su a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye sun kai 3,810
Sojojin Isra'ila sun sake kama wasu Falasdinawa 51 a Yammacin Gabar Kogin Jordan da suka mamaye, inda adadin waɗanda suka kama zuwa yanzu ya kai 3,810 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar wata ƙungiya mai zaman kanta.
A cikin wata sanarwa da kungiyar fursunonin Falasdinu ta fitar ta ce yawancin fursunonin an tsare su ne a birnin Jenin.
A gefe guda kuma sojojin na Isra'ila sun kai farmaki kan garin Silwad da ke gabashin birnin Ramallah tare da yi wa mazauna yankin tambayoyi da dama kafin su sako su, kamar yadda wakilin Anadolu dake wajen ya bayyana.
0132 GMT — MDD ta yi wa Gaza lakabi da 'Jahannama a duniya' yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare
Sojojin Isra'ila sun kai hare-haren bama-bamai a wurare da dama a Zirin Gaza da ake ragargaza a daidai lokacin za a kada kuri'a a babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan wata sabuwar bukatar tsagaita bude wuta.
Sama da wata biyu da fara yaƙin ranar 7 ga Oktoba, babban jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD Philippe Lazzarini, ya kwatanta Gaza da "Jahannama a doron ƙasa".
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji na fargabar yunwa da cututtuka za su mamaye yankin na Falasdinu nan ba da jimawa ba, suna roƙon Isra’ila da ta ƙara ƙaimi wajen kare fararen hula.
1218 GMT — Karacin iskar oxygen ya yi sanadin mutuwar yara uku a asibitin Gaza
Yara uku sun rasu a asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Gaza sakamakon karancin iskar oxygen.
Daraktan asibitin ne ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Sojojin na Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a asibitocin Gaza, inda ko a yau Laraba sai da rahotanni suka ce sojojin sun afka asibitin na Kamal Adwan.
1113 GMT — Mayakan Houthi sun dauki alhakin kai hari kan jirgin ruwan da zai je Isra'ila
‘Yan tawayen Houthi a ranar Talata sun sanar da cewa sun kai hari kan wani jirgin ruwan kasar Norway dauke da man fetur wanda ke hanyar zuwa Isra’ila.
A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar Yahya Saree ya fitar, ya bayyana cewa sun kai wa jirgin ruwan hari ne a Bahar Maliya bayan jirgin ya ki jin gargadin da suka yi.
Yahya ya bayyana cewa akwai jiragen ruwa da dama a kwanakin biyun da suka gabata wadanda suka ji gargadinsu, sai dai a cewarsu, jirgin na kasar Norway ya yi kunnen kashi.
0755 GMT — Jirgin Isra'ila maras matuki ya kashe karin Falasdinawa hudu
Isra’ila ta kashe Falasdinawa hudu a wani hari ta sama da ta kai a birnin Jenin da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye da kuma sansaninta na ‘yan gudun hijira.
Ma’aikatar Lafiya da ke Gaza tare da Kamfanin dillancin labarai na Falasdinu ne suka tabbatar da hakan.
Kamfanin dillancin labaran ya ruwaito cewa akwai karin mutum guda da aka raunata a unguwar al Sibat da ke birnin Jenin.
Daraktan asibitin Jenin ya shaida cewa an kai harin ne kai tsaye kan Falasdinawa. Haka kuma kamfanin dillancin labaran ya tabbatar da cewa sojojin na Isra’ila sun yi wa asibitoci uku kawanya a yankin.
0149 GMT — An kai wa jirgin ruwa hari a Bahar Maliya yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza
Wasu cibiyoyin leken asiri masu zaman kansu sun ce an kai wa wani jirgin ruwa hari a gabar tekun Yemen na Bahar Maliya.
Harin da aka kai kan jirgin ruwan ya zo ne a daidai lokacin da 'yan tawayen Houthi na Yemen ke ci gaba da yin barazana a kan safarar jiragen ruwa na kasuwanci a yankin saboda yaƙin da Isra'ila ke yi a zirin Gaza.
'Yan Houthi dai ba su dauki alhakin kai harin ba, ko da yake kakakin rundunar 'yan tawayen Birgediya Janar Yahya Saree ya ce wata muhimmiyar sanarwa za ta fito daga gare su nan da sa'o'i masu zuwa.
Cibiyoyin leken asiri masu zaman kansu Ambrey da Dryad Global sun tabbatar da cewa harin ya afku ne a kusa da mashigin Bab al-Mandeb da ke raba gabashin Afirka da yankin Larabawa, amma sun ce ba su da wani karin bayani.
Wani makami mai linzami da aka harba daga yankin kasar Yemen da ke karkashin ikon Houthi ya kai hari kan wani jirgin ruwan dakon kaya na kasuwanci, inda ya yi sanadin tashin wuta da jawo ɓarna, kamar yadda jami'an tsaron Amurka biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Wani jami'in ya ce harin da aka kai kan jirgin ruwan na STRINDA ya faru ne daga tazarar kilomita 60 a arewacin gabar tekun Bab al Mandab.
Jami'an sun ce jirgin ruwan Amurka na agaji na Mason ya je wurin kuma yana bayar da agaji. Ba a dai fayyace ko STRINDA na da wata alaka da Isra'ila ko kuma yana kan hanyar zuwa tashar jiragen ruwa ta Isra'ila ba ne.
0134 GMT — A shirye Isra'ila take don sabuwar yarjejeniyar musayar fursunoni da Hamas: Kafafen yada labarai na cikin gida
Isra'ila a shirye take ta dawo da tuntubar masu shiga tsakani domin ganin an sako wasu 'yan Isra'ila da ake tsare da su a Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka rawaito.
Sabuwar yarjejeniyar musayar za a gudanar da ita ne a cikin tsarin sulhu na jinƙai kuma ya haɗa da mata da ke cikin zaman talala da marasa lafiya da waɗanda suka jikkata da kuma tsofaffi, in ji tashar Channel 12 ta Isra'ila.
Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce har yanzu ƙungiyar Hamas na riƙe da fursunoni 137 da suka haɗa da 'yan Isra'ila 126 da 'yan ƙasashen waje 11.
Tashar talabijin ta Channel 12 ta ce jami'an Isra'ila sun yi imanin cewa, ba zai yiwu a cim ma sabuwar yarjejeniyar musayar fursunoni da Hamas a mako mai zuwa ba, amma har yanzu Isra'ila ta yi imanin bude wata sabuwar hanya, ta hancyar cin gajiyar matsin lambar da Hamas ke fuskanta sakamakon yaƙin da ake yi a Gaza da aka yi wa ƙawanya.
Tashar ta rawaito majiyar soji tana cewa tsananin fadan ya fara bude hanyar yin musanyar juna da ba za a rasa ba.
18:07 GMT –– Ɓarnar da aka yi a Gaza ta fi muni fiye da ta Yakin Duniya na II na Jamus — Borrell
Babban jami'in diflomasiyyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya ce halin da ake ciki a Gaza "mummunan bala'i ne, mai ban tsoro", inda ɓarnar da aka samu ta fi wacce aka yi wa Jamsu muni a yaƙin duniya na biyu.
Martanin da sojojin Isra'ila suka yi kan harin Hamas na ranar 7 ga Oktoba ya haifar da "yawan asarar rayukan fararen hula", in ji Borrell a jawabin da ya yi a taron ministocin harkokin wajen EU.
Ya ce EU ta kuma firgita da tashe-tashen hankula a Yammacin Kogin Jordan da masu tsattsauran ra'ayi ke yi, ya kuma yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Isra'ila ta dauka na amincewa da ƙarin wasu gidaje 1,700 a Birnin Kudus, lamarin da Brussels ke ganin ya saba wa dokokin kasa da kasa.