'Yan kasar Haiti na ta gudanar da zanga-zanga kan rashin tsaro a Port-au-Prince. Hoto/ Reuters

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kuri’a inda ya amince da tura sojojin hadin gwiwa zuwa kasar Haiti karkashin jagorancin Kenya domin taimakawa wurin yaki da ‘yan bidniga wadanda suka addabi kasar da ke yankin Caribbean.

An amince da daftarin da Amurka ta bijiro da shi kan lamarin bayan an samu kuri’u 13 da ke goyon bayan tura sojojin, sai kuma biyu ba su yi zabe ba.

Matsayar da aka cimmawa ta bukaci a tura dakaru tsawon shekara daya, inda za a yi bitar ayyukansu bayan watanni tara.

Tura dakarun da za a yi zuwa Haiti a karkashin Majalisar Dinkin Duniya a yanzu shi ne karo na farko a kusan shekara 20.

Ba a saka lokacin da za a tura dakarun ba, duk da cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce akwai yiwuwar tura dakarun tsaro “nan da watanni” zuwa Haiti.

Ranar 1 ga watan Janairun 2024

A wani bangaren kuwa, Ministan Harkokin Wajen Kenya Alfred Mutua ya shaida wa kafar watsa labarai ta BBC cewa ya kamata dakarun su zama suna a Haiti zuwa 1 ga watan Janairun 2023, “ko kafin lokacin.”

Babu tabbaci kan sojoji nawa ake tunanin turawa. Gwamnatin Kenya a baya ta bukaci ta tura ‘yan sanda 1,000. Ko a watan da ya gabata, sai da gwamnatin shugaba Joe Biden ta yi alkawarin tura kayayyaki na kusan dala miliyan 100 domin tallafa wa dakarun Kenya.

Tallafin sojojin waje na da tarihi mai rikitarwa. Majalisar Dinkin Duniya ta soma tura sojojin wanzar da zaman lafiya Haiti a Yunin 2004, inda aka rinka zargin an yin cin zarafi ta hanyar lalata da kuma samun cutar kwalara. Aikin sojojin ya kare a 2007.

Amfani da karfi

Masu caccakar aikin da dakarun Kenya za su je yi a Haiti sun bayyana cewa tun tuni ana zargin ‘yan sandan kasar da ke Gabashin Afirka da azabtarwa da amfani da karfi wanda ya wuce kima da sauran nau’ukan cin zarafi.

Manyan jami’an Kenya sun kai ziyara Haiti a watan Agusta, inda ziyarar ce ta bincike a lokacin da Amurka ke kokarin gabatar da bukatar.

Wannan kuri’ar na zuwa ne kusan shekara guda bayan Firaiministan Haiti Ariel Henry da manyan jami’an gwamnati 18 suka bukaci a tura dakarun kasashen waje cikin kasar a daidai lokacin da gwamnarin kasar ke kokarin dakile kashe-kashen da ‘yan bindiga suke yi da fyade da garkuwa da mutane.

Tun daga 1 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan Agusta, sama da mutum 2,400 aka bayar da rahoton an kashe a Haiti, aka kuma yi garkuwa da sama da 950 sannan aka raunta 902, kamar yadda rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana.

AP