"Hoton allon jefa kuri'a a babban zauren MDD inda ake neman a dauki matakin tsagaita wuta don ayyukan jin kai a Gaza." / Hoto: AFP

Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya shirya amincewa da Falasdinu a matsayin cikakkiyar mambar Majalisar, sannan a tura ƙudirin ga Kwamitin Tsaron MDD don "sake duba batun da kyau".

Falasdinawa na sake dawo da bukatar su ta neman ƙasar ta zama cikakkiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya - matakin da zai tabbatar da Falasdinu ta zama 'yantacciyar kasa - bayan da Amurka ta yi amfani da karfin hawa kujerar na-ƙi a Kwamitin Tsaro na Majalisar mai mambobi 15 a watan jiya.

Jefa kuri'ar da ƙasashen duniya 193 za su yi a Babban Zauren na MDD a ranar Juma'a zai zama wata kuri'ar jin ra'ayin jama'ar duniya don goyon bayan Falasdinu. Bukatar neman zama cikakkiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya na buƙatar amincewar Kwamitin Tsaro sannan Babban Zauren Majalisar.

A yayin da Babban Zaure kaɗai ba zai iya amincewa da ƙasa ta zama cikakkiyar mambar MDD ba, ƙudirin da za a jefa kuri'a a kansa a ranar Juma'a zai ba wa Falasdinawa karin 'yanci da damarmaki daga Satumban 2024 - kmar samun kujera a Babban Zauren MDD tare da sauran kasashe - amma ba za a ba ta damar jefa kuri'a ba.

Jami'an diplomasiyya na cewa akwai yiwuwar ƙudirin ya samu amincewa a Majalisar.

Kokarin falasdinawa na neman ƙasar ta zama cikakkiyar mambar MDD na zuwa ne watanni bakwai da fara yakin Isra'ila a Gaza, kuma a lokacin da Isra'ila ke ƙara faɗaɗa matsugunanta a Yammacin Gabar Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye, wanda MDD ta ce bai halatta ba.

A yanzu Falasdinu na matsayin 'yar kallo a Majalisar Dinkin Duniya, wani mataki mai kama da amincewa da ita a matsayin ƙasa da Babban Zauren ya dauka a 2012.

Kashe kuɗaɗen Amurka

A wata wasika da Wakilan Falasdinu a New York suka aikga zuwa ga ƙasashen duniya mambobin Majalisar Dinkin Duniya a ranar Alhamis, sun an bayyana cewa amincewa da kudirin neman amincewa da Falasdinu ta zama cikakkiyar mambar MDD zai kare batun neman warware rikicin yankin ta hanyar samar da ƙasashe biyu..

Wasikar ta ce goyon bayan zai tabbatar da amincewar karara a wannan lokaci na rudani, ga 'yancin Falasdinawa, ciki har da tabbatar da 'yantacciyar ƙasarsu mai cin gashin kanta."

Tun da jimawa Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ra'ayin wanzuwar kasashe biyu da ke rayuwa daura da juna a kan iyakoki masu tsaro. Falasdinawa na son kasa a Yammacin gabar Kogin Jirdan, da Gabashin birnin Kudus da Gaza, dukkan su yankuna ne da Isra'ila ta mamaye tun 1967 a lokacin da ta gwazba yaƙi da ƙasashen Larabawa.

A farkon makon nan ofishin jakadancin Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa "Har yanzu ra'ayin Amurka shi ne a samarwa da Falasdinawa kasarsu mai 'yanci ta hanyar sulhu da tattaunawa."

Jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya Gilad Erdan a ranar Litinin ya nuna rashin amincewa da kudirin neman baiwa Falasdinu 'yancin zama cikakkiyar kasa mai 'yanci. Ya ce amincewa da kudirin ba zai sauya wani abu ba.

"Idan aka amince da shi, Ina sa ran Amurka za ta dakatar da ɗaukar nauyin ayyukan MDD da hukumominta, kamar yadda dokar Amurka ta tanada," in ji Erdan.

A ƙarƙashin dokokin Amurka. Washington ba za ta iya ɗaukar nauyin duk wata hukuma ta MDD da ta amince da wata kasa da ba ta zama 'yantacciya ba ta zama cikakkiyar mambar Majalisar. A 2011 Amurka ta dakatar da ɗaukar nauyin Hukumar Kula da Ilimi da kimiyya da Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya,UNESCO, bayan da Falasdinu ta zama cikakkiyar mamba a hukumar.

TRT World