Al'ummar ƙasar Iran suna gudanar da zaɓen shugaban ƙasa don maye gurbin Shugaba Ebrahim Raisi wanda ya rasu a watan jiya a wani haɗarin jirgin helikwafta. 'Yan takara huɗu ne suke fafatawa daga taƙaitaccen jerin waɗanda ke biyayya ga shugaban addini na ƙasar.
An buɗe rumfunan zaɓe da ƙarfe 04:30 agogon GMT, kuma za a rufe su da ƙarfe 2 da rabi na rana agogon GMT ranar Juma'a, duk da an saba ganin ana jinkirtawa har zuwa tsakar dare.
Yayin da ake ƙirga ƙuri'u da hannu, ana sa ran sanar da sakamakon zaɓen cikin kwanaki biyu, duk da za a iya samun sakamakon farko da wuri.
Duk da dai ana ganin zaɓen ba zai kawo wani babban sauyi ba a tsare-tsaren ƙasar, sakamakonsa zai iya shafar tantance wanda zai gaji Ali Khamenei, shugaban Addini na Iran wanda yake da shekaru 85, kuma yake kan mulki tsawon shekara 35.
Khamenei ya yi kiran da a yi "gangamin fitowo" zaɓen don kawar da tababa kan sahihancin zaɓen, sakamakon damuwar da mutane ke da shi saboda matsin tattalin arziƙi da tsuke 'yancin siyasa da tattalin arziƙi.
Yawan masu fitowa zaɓe ya ragu cikin shekaru huɗu da suka gabata, inda yawancin matasa suka ƙosa da tsuke fagen siyasa da zamantakewa.
Idan babu ɗan takarar da ya ci aƙalla kashi 50 da ƙarin ƙuri'a ɗaya na ƙuri'u da aka kaɗa, ciki har da ƙuri'un da babu suna, to za a je zagaye na biyu tsakanin waɗanda ke kan gaba, ranar Juma'ar farko bayan sanar da sakamakon zaɓen.
Tsamarin tunzuri a yankin
Zaɓen na Iran na faruwa ne yayin da ake samun ƙarancin masu fita zaɓe. Kashi 48 na masu zaɓe ne kaɗai suka fito zaɓen 2021, wanda Raisi ya lashe. Sannan yawan fita zaɓe ya ƙara raguwa ƙasa zuwa kashi 41 a zaɓen 'yan majalisa watanni uku da suka gabata.
Wannan zaɓen ya zo lokacin da ake samun ƙaruwar takun-saƙa a yankin sakamakon yaƙin da Isra'ila take kan Gaza da Lebanon, da kuma cigaban matsin lamba kan Iran dangane da shirinta na makamin nukiliya da yake kankama.
Shaharrare cikin 'yan takarar shi ne Mohammad Baqer Qalibaf, kakakin majalisa, kuma tsohon magajin-garin Tehran, sai kuma Saeed Jalili, tsohon mai shiga tsakani a tattaunawar nukiliya wanda ya yi aiki na shekara huɗu a ofishin Khamenei.
Sai kuma Massoud Pezeshkian, wanda ke goyon bayan tsarin jagorancin ƙasar bisa doron addini, amma yana neman sassauta tsamin dangantaka da ƙasashen Yamma, da kawo sauyin tattalin arziƙi, da faɗaɗa fagen siyasa da zamantakewa.
Duka 'yan takarar huɗu sun sha alwashin farfaɗo da tattalin arziƙi, wanda ke fama da rauni, da kawo ƙarshen almundahana a mulki, da takunkumin da aka ƙaƙaba wa ƙasar tun 2018, bayan Amurka ta yi watsi da yarjejeniya kan nukiliya ta 2015 tare da manyan ƙasashe shida na duniya.