Yayin da yake rage watanni biyar kafin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Amurka, manyan 'yan takarar shugabancin ƙasar, Shugaba mai ci, Joe Biden, da tsohon Shugaba, Donald Trump sun tafka muhawararsu ta farko a birnin Atalanta na jihar Florida.
'Yan siyasar yi cacar-baki kuma sun riƙa zargin junansu da yin ƙarerayi yayin da suke tattauna batun manufofin harkokin wajen ƙasar, da tattalin arziƙi da batun zubar da ciki.
Ana kallon wannan zazzafar karawar da dattijan 'yan takarar suka yi a matsayin manuniya kan yadda babban zaɓen watan Nuwamba mai zuwa zai kasance mai zafi.
Trump ya soki Biden kan tattalin arziƙi da kuma tsare-tsaren manufofin harkokin wajensa, yayin da Biden ya taɓo batun laifin da kotu ta samu Trump da shi da kuma batun yunƙurin da ya yi na juya sakamakon zaɓen shekarar 2020.
Dattijan 'yan siyasar biyu, waɗanda suka riƙa zagin juna, su ne mutanen da suka fi tsufa da suke neman shugabancin Amurka da aka taɓa gani a tarihin ƙasar.
Mutanen biyu sun yi muhawara mai zafi kan dokokin zubar da jiki da batun kwararar baƙi, da batun yaƙin Ukraine da na Gaza, da kuma batun tafiyar da tattalin arziƙi da na wasan Golf da kowanensu ke bugawa.
Saboda yadda ƙwazon ’yan siyasar biyu ya bambanta yayin muhawarar, gwiwoyin wasu ’yan jam’iyyar Democratic sun fara yin sanyi, kuma hakan zai sa wasu masu kaɗa ƙuri’a su fara nuna damuwa kan cewa Biden, mai shekara 81, tsufansa zai kawo tangarɗa ga nasarar sabon wa’adin mulkinsa.
Wani babban mai bai wa Biden gudunmuwar kuɗin kamfe, wanda ba ya so a bayyana sunansa, ya soki shugaban kuma ya ce muhawarar ta nuna “bai cancanta ba”. Haka nan ya ce yana sa ran cewa za a fara sabon kiraye-kiraye kan ka da Biden ya sake yin takara gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa a watan Agusta.
Daga bisani Mataimakiyar Shugaban Ƙasar, Kamala Harris ta amince cewa Biden ya fara muhimmiyar muhawarar “babu karsashi”, inda ya fafata da babban abokin hamayyarsa, ko da yake ta ce jam’iyyarsu ta Democratic ta gama muhawarar da “ƙarfin gwiwa.”
“Ya fara babu karsashi wanda kowa ya san haka. Ba zan iya kare wannan ba,” kamar yadda ta bayyana wa kafar yaɗa labarai ta CNN, bayan muhawarar da Biden ya nuna rashin karsashi kuma ya sanya shakku a zukatan jama’a kan sake tsayawarsa takara.
Za a sake yin muhawara ta biyu kuma ta ƙarshe tsakanin manyan ’yan takarar biyu a watan Satumba mai zuwa.
A watan Nuwamba ne za a gudanar da babban zaɓe a Amurka, kuma Shugaba Biden ne ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyyar Democratic, yayin da tsohon Shugaba Trump yake yi wa babbar jam’iyyar adawa ta Republican takara.