Lardin Sistan-Baluchestan, da ke kan iyaka da Pakistan yana kudu maso gabashin Iran. / Hoto: TRT World

Aƙalla jami'an tsaro uku sun mutu a wasu hare-hare da aka kai a lokaci guda a sansanonin soji da lardin Sistan and Baluchestan da ke kudu maso gabashin Iran, a cewar kafofin watsa labarai da jami'an gwamnatin ƙasar.

Kamfanin dillancin labarai na IRNA, wanda ya ambato wasu majiyoyi suna tabbatar da kai hare-haren, ya ce an kai "hare-haren ta'addanci guda uku" a lokaci guda a sanyin safiyar Alhamis a ofishin ƴan sanda da kuma sansanonin soji guda biyu a babban irnin Chabahar da kuma birnin Rask.

IRNA ya ce an jikkata aƙalla mahara uku tare da kashe ɗaya a wani martani da ƴan sanda suka mayar. Ana ci gaba da farautar maharan, in ji IRNA.

An kashe jami'an tsaro aƙalla uku yayin hare-haren, a cewar kafofin watsa labarai na ƙasar. Rahoton IRNA bai bayyana ɓarnar da aka yi wa ƴan sanda ba, sai dai rahotanni sun ce mai yiwuwa an tafka musu mummunar ɓarna.

IRNA da wasu kafofin watsa labaran Iran sun ambato mataimakin gwamnan lardin yana cewa wani mahari ya yi yunƙurin shiga hedkwatar Rundunar Juyin-Juya-Hali ta Islamic Revolutionary Guard Corps ( IRGC) da ke Rask amma an hana shi.

"A ƴan mintocin da suka wuce, ƴan ta'adda sun kai hari a hedkwatar sojoji da ke Rask da Chabahar. An ɗauki matakin kan lamarin kuma za a bayar da cikakiyar sanarwa game da batun nan gaba," in ji Ali Reza Merhameti.

TRT World