Talata, 8 ga watan Oktoba, 2024
1350 GMT — Akalla sojojin Isra'ila 48 ne suka jikkata a Gaza da Lebanon cikin sa'o'i 24 da suka gabata, kamar yadda shafin intanet na rundunar sojojin Isra'ila ya bayyana.
Isra'ila ta zafafa kai hare-hare ta kasa a gabar tekun kudancin Lebanon, inda ta tura karin sojoji tare da yin kira ga fararen hula da ke kusa da Tekun Bahar Rum da su ƙaurace wa gidajensu.
Kungiyar Hezbollah ta ce ta harba makami mai linzami a birnin Haifa na Isra'ila bayan da sojojin Isra'ila suka bayar da rahoton cewa an harba makamai 85 daga Lebanon.
0911 GMT — Hukumomin MDD sun yi gargadi game da ƙarancin abinci da ɓarkewar cututtuka a Lebanon
Hukumar Samar da Abinci ta Duniya ta bayyana damuwarta kan yadda kasar Lebanon ke samun matsalar iya ciyar da kanta, yana mai cewa an lalata ko kuma watsi da dubban kadada na gonaki a kudancin kasar saboda hare-haren Isra'ila.
Mathew Hollingworth, darektan WFP na kasar Lebanon, ya shaida wa taron manema labarai a Geneva cewa, "Hakika noma, samar da abinci, akwai damuwa mai ban mamaki ga samun damar Lebanon na ci gaba da ciyar da kanta," yana rubewa a gonaki.
A wajen taron, jami’in Hukumar Lafiya ta Duniya Ian Clarke a birnin Beirut ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar barkewar cututtuka a tsakanin al’ummar Lebanon da suka rasa matsugunansu.
"Muna fuskantar wani yanayi inda ake fuskantar barazanar barkewar cututtuka, kamar zazzabi da gudawa mai saurin kisa da hepatitis A, da wasu cututtukan da za a iya rigakafin rigakafin," in ji Clarke.
0700 GMT — Isra'ila ta tura ƙarin dakaru Lebanon, ta faɗaɗa yaƙi zuwa kudu maso yammacin ƙasar
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta tura "ƙarin dakaru" zuwa kudu masu yammacin Lebanon.
"Runduna ta 146 ta tura ƙarin dakaru zuwa kudancin Lebanon a wani ɓangare na ci gaba da yaƙi da Hezbollah," a cewar wani saƙo da ta wallafa a Telegram.
Waɗannan dakaru na ko-ta-kwana za su bi sahun sauran dakaru na rundunoni uku —runduna ta 98 da ta 36 da kuma ta 91 — waɗanda aka tura kudancin Lebanon, a cewar jaridar Times of Israel.
Jarudar ta ruwaito cewa hakan ya ƙara adadin dakarun Isra;ila da ke yaƙi ta ƙasa a Lebanon zuwa fiye da 15,000
0452 GMT — Isra'ila ta yi iƙirarin kashe wani babban kwamandan Hezbollah a Beirut
Rundunar sojojin Isra'ila ta yi iƙararin kashe Suhail Hussein Husseini, wani babban kwamadan Hezbollah, a wani hari da ta kai Beirut.
Rundunar sojin ta ce Husseini ya taka muhimmiyar rawa wajen aika makamai daga Iran zuwa ƙasar da kuma rarraba su ga mayaƙan Hezbollah.
Bugu da kari, an ce yana da hannu wajen tsare-tsare na harkokin kuɗi da tafiyar da sauran manyan ayyukan ƙungiyar.
Kawo yanzu dai Hezbollah ba ta ce komai a kan wannan iƙirari ba.
A nata ɓangaren, Hezbollah ta yi iƙararin harba makamai masu linzami a tashar jiragen ruwa ta Isra'ila a birnin Haifa da kuma sansanin sojojin Isra'ila da ke da birnin Tel Aviv ranar Talata.
2052 GMT — Amurka ta gargaɗi Isra'ila kada ta kai hari a filin jiagen saman Beirut
Amurka ta gargaɗi Isra'ila kada ta kai hari a filin jiragen saman Beirut ko kuma hanyoyin da ake bi domin isa filin, a yayin da sojojin Isra'ila suka kai manyan hare-hare a yankunan da ke bayan babban birnin na Lebanon.
"Muna gani yana da matuƙar muhimmanci filin jiragen saman ya kasance a buɗe, yana kuma da muhimmanci hanyoyin da ake isa filin su zama suna aiki, ta yadda Amurkawa da ke son barin yankin za su samu damar bari, kuma su ma 'yan sauran ƙasashe za su samu damar barin yankin," in ji kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Matthew Miller a hira da manema labarai.
2050 GMT — Hezbollah ta kai hari a cibiyar tattara bayanan sirri da ke Tel Aviv
Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta ce ta kai hari da wani makami mai linzami kan cibiyar tattara bayanan sirri da ke gefen birnin Tel Aviv.
2038 GMT — Isra'ila ta ce an harba mata makamai biyar daga Lebanon
Rundunar sojojin Isra'ila ta ce an harba mata aƙalla makamai biyar daga Lebanon, ko da yake ta kakkaɓo wasu daga cikinsu.
"Bayan jiniya ta yi ƙara a wasu yankuna da ke tsakiyar Isra'ila, an gano makamai biyar da aka harbo daga Lebanon zuwa cikin Isra'ila," a cewar wata sanarwa da rundunar sojojin Isra'ila ta fitar.
"Rundunar sojojin sama ta IAF ta kakkaɓo wasu daga cikinsu, yayin da sauran suka sauka a fili (inda babu mutane)."