Isra'ila na ci gaba da kashe farar hula a Gaza waɗanda akasarinsu mata ne da yara. / Hoto: AA

0851 GMT — Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce ya ga wasu “alamu masu bayar da ƙwarin gwiwa” game da ci gaban da aka samu ta fannin tsagaita wuta a Gaza.

Maganganun nasa na zuwa ne bayan tattaunawarsa da Sakataren Harkokin Wajem Turkiyya Hakan Fidan dangane da zuwansa Syria a karo na biyu bayan rushewar gwamnatin Bashar al-Assad.

“Mun tattauna a kan Gaza, kuma ina ganin mun tattauna kan...yiwuwar samun yarjejeniyar tsagaita wuta. Haka kuma abin da muka gani a makonnin da suka gabata wasu alamu ne da ke nuna cewa akwai yiwuwar samun hakan,” kamar yadda Blinken ya shaida wa manema labarai a Ankara

0756 GMT — Falasdinawa uku ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan wani tanti da ya kasance mafaka ga waɗanda suka rasa muhallansu a garin Khan Younis da ke kudancin Gaza.

Majiyoyin lafiya sun ce harin ta sama ya afka wa wani tanti da ke ɗauke da iyalan Jabour da suka rasa matsugunansu a yankin Jouret Al Lout da ke kudancin Khan Younis.

A tsakiyar Gaza, shaidu sun bayyana cewa, Isra'ila ta kai hare-hare kan fararen hula a kusa da kungiyar mata a sansanin Nuseirat, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Likitoci sun kuma tabbatar da jikkatar wasu mutane sakamakon harin da da jirgi ya kai a wani gida da ke kusa da masallacin Yassin a yankin.

2100 GMT —Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 30 a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke Gaza

Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla 30 tare da jikkata 40 a harin da ta kai ta sama a wani gida da ke sansanin Nuseirat da ke Gaza da aka yi wa kawanya.

Jiragen yakin Isra'ila sun kai hari kan gidaje da gine-gine da dama a sansanin, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Falasdinu WAFA ya ruwaito.

Rahotanni sun nuna cewa akasarin wadanda aka kashe da kuma jikkata mata ne da kananan yara.

Shaidu sun bayar da rahoton barna sosai a yankin, inda motocin daukar marasa lafiya da jami’an tsaro suka ci gaba da neman mutanen da suka bace a karkashin baraguzan ginin.

Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a kullum waɗanda akasarinsu yara ne da mata. / Hoto: / Photo: AA

2048 GMT Dakarun Isra'ila sun tare ayarin motocin Majalisar Dinkin Duniya dauke da man fetur da kayayyakin kiwon lafiya da nufin tallafawa asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Gaza, in ji darektan asibitin.

A cikin wata sanarwa ta bidiyo, Hussam Abu Safiya ya ce tawagar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da mu cewa, sojojin Isra'ila sun hana ayarin motocin da ke dauke da man fetur da magunguna masu muhimmanci shiga, lamarin da ya tilasta musu komawa kudancin Gaza.

Da yake karin haske kan halin da ake ciki, ya ce: "Akwai matukar karancin kayayyakin jinya da ake bukata don jinyar wadanda suka jikkata da ke isa asibiti. Muna gudanar da ayyuka kaɗan-kaɗan saboda ƙarancin kayan aiki."

TRT Afrika da abokan hulda