Isra'ila ba ta mayar da martani ba game da zargin yin leken asiri. / Hoto: AA Archive

Da yake yin martani game da kama mutum 33 bisa zarginsu da yin leken asiri a madadin hukumar leken asirin Isra'ila ta Mossad, Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya jaddada gargadin da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi cewa Isra'ila za ta "dandana kudarta" idan ta yi leken asiri a Turkiyya.

Erdogan ya yi gargadin ne a watan jiya bayan Ronen Bar, shugaban hukumar leken asirin ciki gida ta Isra'ila Shin Bet, ya ce kasarsa ta tsara wasu shirye-shirye na halaka mambobin kungiyar Hamas da ke zaune a kasashen waje.

"Idan suka kuskura suka dauki wannan mataki a kan Turkiyya da al'ummarta, za su dandana kudarsu kuma za su fuskanci yanayin da ba za su warware daga gare shi ba," in ji Erdogan.

Bayan kamen da aka yi kwanakin baya a Istanbul, ranar Talata Daraktan Sadarwar Altun ya wallafa sakon Erdogan na watan jiya a shafin X, yana jaddada gargadi ga hukumomin Isra'ila cewa kada su yi yunkurin gudanar da wannan danyen aiki a Turkiyya.

"Ba su san Turkiyya ba, ba su san mutanen Turkiyya ba. Yin wannan kuskure zai jaza musu bala'i. Idan suka kuskura suka dauki irin wannan mataki a Turkiyya, za su gane kuskurensu yadda ba za su wartsake ba; za su gamu da fushinmu, in ji Erdogan a hira da manema labarai ranar 6 ga watan Disamba.

"Ya kamata masu son yin wannan aiki su sani cewa za su dandana kudarsu. An san kwarewar Turkiyya a fannin leken asiri da tsaro a duk fadin duniya. Sannan kuma, mu ba yau aka kafa mu ba," in ji shi.

Leken asiri na duniya

An yi kamen na ranar Talata ne bayan wani bincike da Ofishin Mai Shigar da Kara kan Ta'addanci da Manyan Laifuka da ke Istanbul ya yi kan masu leken asiri na kaasshen duniya.

Ana zargin mutanen da yin kutse a harkokin tsaro da kai hari da sace mutane a madadin Mossad.

An gudanar da samame a wurare 57 da ke larduna takwas inda aka kama mutanen, yayin da kuma yanzu haka ake neman mutum 13.

Hukumomin da suka yi samamen na hadin gwiwa sun hada da Hukumar Leken Asiri ta (MIT) da Rundunar 'yan sandan Istanbul, inda suka kama mutanen da ake zargi. Mutanen da ake zargi sun yi sojan-gona ne a matsayin ma'aikatan wani kamfani da ke wajen Istanbul, inda suke tatsar bayanai game da Falasdinawa da ke Turkiyya suna bai wa Mossad domin samun kudi.

TRT World