Alƙalan Kotun Duniya a yayin da suke barin harabar kotun bayan kammala yanke hukunci dangane da mamayar da Isra'ila ta yi wa Falasɗinaws. / Hoto: AFP

Daga Hassan Ben Imran

A makon da ya gabata, Kotun Duniya, wadda ita ce Kotun Koli ta Duniya, ta gabatar da wani muhimmin hukunci na tarihi inda ta ayyana mamayar da aka yi wa sassan Falasɗinu tun daga 1967 a matsayin ba kan ka'ida ba.

Wannan hukuncin ya ƙara jaddada damar da Falasɗinawa suke da ita ta 'yancinsu, daga ciki har da 'yancin komawa wurarensu da biyansu diyya.

A hanyoyi da dama, hukuncin ya kasance wani babban labari ga gwagwarmayar da Falasɗinawa suke yi.

Sai dai tun bayan da aka yanke wannan hukuncin, na sha tambayoyi daga abokan aikina masu yawa da 'yan jarida a kan ba wai abin da nake tunani kawai ba, amma yadda nake ji game da shi.

Ya kunshi jin abubuwa da yawa. Wani hukunci ne na ci gaba kuma na taimako, la'akari da gazawar tsarin da bai dace ba, amma farashin wannan hukuncin jinin Falasdinawa ne ya biya.

Abin da kotun ta ce

Ba shakka Kotun Duniya ta ayyana mamayar da Isra'ila ta yi wa Falasɗinawa a matsayin wadda aka yi ta ba bisa ƙa'ida ba, wanda hakan ke nufin akwai buƙatar mamayar ta dakata sannan masu mamayar su tashi daga garuruwan da suka mamaye.

Kotun ta ci gaba da nanata cewa, Isra'ila tana mamaye yankunan Falasdinawa ba bisa ka'ida ba, tana kuma nuna wa Falasdinawa wariyar launin fata.

Akwai misalai da aka bayar game da wariyar launin fatar a sashi na 3 na kundin kotun dangane da kawar da duk wasu matakai na nuna wariyar launin fata (ICERD). Wannan babban abu ne.

Sashe na 3 na ICERD kai tsaye na magana ne dangane da ƙasashe su yi Allah wadai da hani da kawar da duk irin waɗannan lamura. Wannan ne ya bai wa ƙasashe amfani da dama iri-iri domin matsin lamba ga Isra'ila domin ta bi doka.

A mabambanta ra'ayoyinsu da suka bayyana, alkalai Nawaf Salam da Dire TIadi sun tabbatar da hakan. Alƙali Tladi wanda ya taɓa fuskantar wariyar launin fata, wanda ya kawo misali da Afirka ta Kudu.

Kotun ta kuma ce ba za a iya ba da misali da yarjejeniyar Oslo ko amfani da ita wajen tauye hakkin Falasdinawa ko kuma tauye hakkin Isra'ila.

Hukuncin ya yi nuni da sashi na 47 na Yarjejeniyar Geneva ta IV, wadda a cikinta "ba za a tauye haƙƙin mutanen da ke da kariya a yankin da aka mamaye ba… daga fa'idar Yarjejeniyar yanzu ta… duk wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin hukumomin yankunan da aka mamaye da kuma mai mamayar, ko kuma yadda mai mamayar ta mamaye duk wani sashe na yankin."

Ra'ayoyi daban-daban dangane da hukuncin kotun, wanda alƙalan daban-daban suka yi, a wani lokacin sun fi ƙarfi.

Alƙali Salam, a ra'ayinsa na daban, ya bayyana cewa take haƙƙin Falasɗinawa ya samo asali ne tun daga shekarar 1948, shekarar Nakba da kuma kafa ƙasar Isra'ila, ba wai a 1967 kaɗai ba.

A iya sani na, wannan ne karo na farko a shari'ance da aka yi magana a kan Nakba, duk da cewa ba a yi amfani da kalmar ba a matakin na shari'a.

Alƙali Abdulqawi Yusuf da Xue Hanqin duka suna da ra'ayoyi daban-daban kan hakan inda suke da ra'ayi ne kan mulkin mallaka ba wai batu na mamaya ba.

Mamayar Isra'ila da kuma kare kai

Ayyana haramta mamaya na nufin ci gaba da mamayar kuma wani nau'i nata na nufin aikin zalunci.

Wannan yana da sakamako kai tsaye kan iƙirarin da Isra'ila ke yi na kare kai. Idan ƙasa ta mamaye wani yanki ba bisa ka'ida ba, a hakan tana cikin aikata zalunci, a matsayinta na wadda ta soma zaluncin, ba ta da wata hujja ta kare kai.

Mutane da yawa za su yi da’awar cewa Isra’ila ba ta taɓa samun ‘yancin kare kai daga hare-hare daga yankin da ta mamaye ba, ko da kuwa matsayin wannan mamaya ne. Ko ta yaya, ya kamata a warware wannan muhawara sau ɗaya kuma gaba ɗaya.

Tattaunawa da yarjejeniyar Oslo

Kotun ta kara yin magana game da yarjejeniyar Oslo da Isra'ila ta yi amfani da ita da gangan don kawar da hankalin Falasdinu daga keta haddin da ta yi, da kuma nuna shakku kan ikon Falasdinu na shiga Majalisar Dinkin Duniya ko gabatar da wata bukata a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.

Hukuncin na ICJ ya jaddada cewa yarjejeniyar Oslo, yarjejeniyoyin farko tsakanin PLO da Isra'ila a shekarun 1990, ba za su iya kawar da haƙƙin Falasɗinawa ba ko kuma tauye haƙƙin Isra'ila.

Ya kamata gwamnatin Birtaniya ta ji wannan karara, wadda ta ƙalubalanci ikon kotun na ICC dangane da hakan.

ICC da kanta ya kamata ta lura da hakan kuma ta hana Birtaniya, ko kuma wata ƙungiya, daga rashin amincewa da ikonta a kan haka.

Kan batun tattaunawar nan gaba, idan ana ganin hakan zai yiwu, bayan an ayyana mamayar a matsayin wadda ba bisa ƙa'ida ba, hakan na nufin abubuwan da suka ƙunshi wuraren 'yan kama wuri-zauna ba za su ci gaba da zama abubuwan da za a tattauna a kan teburin sulhun ba.

Abubuwan da aka kafa bisa doka ba za a iya siyasantar da su ba. Kafin a soma duk wata tattaunawa, akwai buƙatar a yi batun ɗaukar matakai domin kawo ƙarshen mamaya.

Don haka, sakamakonsa kamar ƙauyukan 'yan kama wuri zauna a waragaza su baki ɗaya har da na Gabashin Birnin Kudus.

Wariyar launin fata da mulkin mallaka

Kan batun wariyar launin fata, waɗanda suke ƙalubalantar Isra'ila kan cewa ƙasa ce mai nuna wariyar launin fata akwai jan aiki a gabansu kan dalilin da ba su bayyana ta a matsayin ƙasa mai nuna wariyar launin fata ba.

Bayan samun rahotanni da dama daga Majalisar Ɗinkin Duniya da wasu manyan ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama na Falasɗinu da Isra'ila, sun tabbatar da wannan ayyanawar, yawancin muryoyi, musamman daga cikin Tarayyar Turai da Arewacin Amurka, sun magantu don kare Isra'ila tare da haɓaka ma'anar nuna ƙyama, inda rahotanni suka nuna cewa Isra'ilar ta buƙaci a hukunta wanda ya dangantata da wariyar launin fata.

Yanzu dole ne su bayyana kansu dangane da hukuncin da babbar kotun duniya ta yanke.

A ƙarshe kotun, ta hanyar ƙin amfani da wannan kalmar a hukuncin da ta yanke, sai ta faɗi a bayyane cewa Isra'ila tana aikata abin da ake kira "kama wuri-zauna na mulkin mallaka". Wannan na daga cikin abin da a bayyane alƙalai Xue da Yusuf suka bayyana.

TRT World