1747 GMT — Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a harin da ta kai sansanin 'yan gudun hijira na Al Mawasi ya ƙaru zuwa 90, kuma rabinsu mata ne da yara, sannan mutum sama da 300 sun jikkata, a cewar Ma'aikatar kiwon lafiya ta Gaza.
1716 GMT — Ƙasashen Yamma za su ci gaba da goyon bayan yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza saboda 'abin kunyar nan' na kisan kiyashi: Erdogan
Ƙasashen Yamma za su ci gaba da goyon bayan yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza babu ƙaƙƙautawa duk kuwa da cewa hakan ya saɓa wa dokokinsu, “kuma hakan yana faruwa ne saboda abin kunyar nan" na 'yan Nazi wato kisan kiyashi, in ji shugaban Turkiyya.
“Idan ban da tsirarun mutane masu ƙima” da suka nuna damuwa kan lamarin, amma galibin kafofin watsa labaran Yamma ba su mayar da hare-haren da Isra'ila ta kwashe watanni tara tana kai wa Gaza a matsayin wani abu mai muhimmanci ba, a cewar Recep Tayyip Erdogan, inda ya ƙara da cewa: “Sun kawar da kai daga kisan kiyashin da ke faruwa, sun yi watsi da koke-koken mutanen da aka danne.”
Erdogan ya caccaki ƙasashen Musulmai saboda gaza yin kataɓus kan bala'in da ke faruwa a Gaza, yana mai cewa ƙungiyoyin ƙasashen Musulmai da ma na duniya sun “gaza ɗaukar mataki kan lamarin Gaza.”
“A yayin da ya dace ƙasashen Musulmai su caccaki ƙasashen Yamma kan kisan ƙare-dangin Gaza, na yi ammana ya kama su ma su tuhumi kawunansu,” in ji Erdogan.
“Ban ga dalilin da zai sa ƙasashen Musulmai su kasa ɗaukar mataki kan Isra'ila ba, ganin cewa muna da al'umma da suka wuce biliyan 2, sannan muna da ƙarfin tattalin arziki na tiriliyoyin dala,” kamar yadda ya ƙara da cewa.
1001 GMT — Akalla Falasdinawa 71 ne aka kashe tare da jikkata wasu sama da 289 a wani harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijira a kudancin Gaza.
Sanarwar Ma'aikatar Lafiya ta ba da sabuwar ƙididdigar "adadin kisan gillar da Isra'ila ta yi" a sansanin Al Mawasi, daga aƙalla 20 da ta ce da farko an kashe.
Tun da farko a cikin wata sanarwa da ma'aikatar lafiya ta Gaza ta fitar ta ce "gawawwakin Falasɗinawa 20 da kuma fiye da 90 da suka jikkata sun isa cibiyar kula da lafiya ta Nasser da ke Khan Younis bayan da sojojin Isra'ila suka yi ruwan bama-bamai a yankin Al Mawasi da ke yammacin Khan Younis a kudancin zirin Gaza."
Wasu da suka shaida lamarin sun bayyana wa kamfanin dillancin labaran Anadolu cewa, sojojin na Isra'ila sun yi amfani da manyan makamai masu linzami guda biyar, wajen kai hari a yankin Al Mawasi, wanda sojojin Isra'ila a baya suka ayyana a matsayin wani yanki mai aminci.
0305 GMT — Wakilin Falasɗinu na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya Riyad Mansour ya jaddada cewa Isra’ila na ci gaba da raba Falasɗinawa da muhallansu a Gaza a kullum.
“Muna sake kira, cikin gaggawa, ga ƙasashen duniya da su dakatar da Isra’ila daga kisan da take yi wa jama’ar Falasɗinawa,” kamar yadda Mansour ya rubuta a wani roƙo da ya aika wa shugabannin duniya.
Mansour ya sake jaddada cewa “ana ci gaba da tilasata wa farar hula barin muhallansu a faɗin Gaza bisa rashin mutunci da rashin bin doka, wanda ke haifar da tarzoma da rudani, musamman ga yara da sauran fararen hula masu rauni, ciki har da marasa lafiya, da waɗanda suka jikkata da nakasassu."
2117 GMT — Kafofin watsa labarai a Isra'ila sun ambato wasu majiyoyi da ke cewa Firaminista Benjamin Netanyahu kusan shi kaɗai yake yin kiɗansa, sannan ya yi rawarsa a tattaunawar da ake yi da ƙungiyoyin fafatukar kare Falasɗinawa game da musayar fursunonin da Isra'ila ke tsare da su da kuma Isra'ilawa da aka yi garkuwa da su.
Kafar watsa labarai ta gwamnatin Isra'ila KAN ta ambato wasu majiyoyi da ba sa so a ambaci sunayensu suna cewa Netanyahu shi kaɗai yake tattaunawa da sauran ɓangarorin, kuma ya yanke shawarar ƙin sassauta ra'ayinsa.
Netanyahu ne yake jagorantar dukkan tattaunawar da ake yi, kuma ya mayar da hankali a kan tattaunawar fiye da yadda ya yi a baya, in ji majiyoyin.
Ita ma jaridar Yedioth Ahronoth ta ce ana fargabar cewa Netanyahu yana ƙoƙarin kawo cikas a game da tattaunawa kan musayar fursunonin bayan ya samu rashin jituwa da shugaban hukumar leƙen asirin ƙasar Mossad, David Barnea, a kan wasu daga cikin sharuɗɗan tattaunawar.
Ta ƙara da cewa ɗaya daga cikin manyan bambance-bambancen da ke tsakanin Netanyahu da Mossad da kuma hukumar tsaron Isra'ila, Shin Bet, shi ne hukumomin tsaron ba su amince a koma fagen yaƙi ba sai idan Hamas ta keta sharuɗɗan jarjejeniyar, yayin da shi kuma yake so a ci gaba da yaƙi ko da kuwa mai zai faru.
2108 GMT — Sanata Bernie Sanders ya yi kira ga Amurkawa kada su kawar da kai daga yaƙin Gaza
Sanata Bernie Sanders ya yi kira ga al'ummar Amurka da kada su bari guguwar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar ta kawar da hankulansu daga babban bala'in da ke faruwa a Gaza.
"A yayin da yawancin kafofin watsa labarai suka mayar da hankali kan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar Amurka, dole ne mu ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a Gaza, inda mutane suke ci gaba da fuskantar bala'i da rashin jinƙai," a cewar wata sanarwa da Sanders ya fitar.
Sanders ya ƙara da cewa Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi kan Falasɗinawan Gaza ba tare da sassauci ba, yana mai zargin cewa Firaminista Benjamin Netanyahu "ya yi watsi da dukkan dokokin ƙasashen duniya sannan ya jefa rayuwar al'ummar Gaza cikin masifa".
"Shi ya sa Netanyahu yake fuskantar tuhuma daa Kotun Hukunta Manyan Laifka ta Duniya," in ji Sanders.
Sanatan wanda ke takara a matsayin ɗan indifenda ya ce Amurka tana ci gaba da kashe biiliyoyin dala don taimaka wa Isra'ila sannan tana ba ta bama-bamai da makamai don ci gaba da yaƙi a Gaza.
"Mu, Amurkawa, muna da laifi a wannan ta'asa," in ji Sanders, sannan ya yi kira ga Amurka ta daina taimaka wa "yaƙin da Netanyahu yake yi".