Littafi mai taken "Recep Tayyip Erdogan’s Peace Diplomacy: The Case of Syria," ya bayyana rawar da Turkiyya ta taka ƙarƙashin jagorancin Shugaba Erdogan ta yin amfani da hanyoyin zaman lafiya da adalci da wanzar da zaman lafiya a Syria. . / Photo: AA Archive

Ma'aikatar Sadarwa ta Fadar shugaban ƙasar Turkiyya ta sanar da ƙaddamar da sabon littafi mai taken "Recep Tayyip Erdogan’s Peace Diplomacy: The Case of Syria," wanda ya bayyana irin rawar da Turkiyya ta taka a fannin diflomasiyya domin kawo ƙarshen yaƙin basasar shekaru 13 a Syria.

Littafin, wanda aka wallafa a harshen Turkanci da Larabci da Turanci, ya bayyana rawar da Turkiyya ta taka ƙarƙashin jagorancin Shugaba Erdogan ta yin amfani da hanyoyin zaman lafiya da adalci da wanzar da zaman lafiya a Syria.

Ranar Alhamis Darakta Sadarwa Fahrettin Altun ya bayyana ƙaddamar da wannan littafi a saƙon da ya wallafa a shafin X, inda ya jaddada matsayin Turkiyya na tabbatar da 'yancin Syria a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta da haɗin kai a fannin siyasa da kuma 'yancin al'ummar Syria na jajircewa domin gina ƙasarsu.

Ya ƙara da cewa a koyaushe Turkiyya za ta goyi bayan gaskiya da adalci a yayin da Syria ke fama da matsala ta rashin jinƙai.

Tun da aka soma rikici a Syria, Turkiyya ta aiwatar da matakai na samar da agajin jinƙai, inda ta bayar da mafaka ga miliyoyin 'yan ƙasar Syria tare da yaƙi da ƙungiyoyin 'yan ta'adda da ke barazana ga tsaron ƙasar.

Littafin ya bayyana ƙoƙarin Turkiyya ta hanyar diflomasiyya, ciki har da samar da mafita ta hanyoyin zaman lafiya da adalci da 'yanci, tare da yin la'akari da tsarin "Ƙasar Syria ta 'yan Syria ce."

TRT World