An dauki tsawon shekaru sama da 100 ana gudanar da zabuka a Turkiyya / Hoto: AA

A lokacin da ‘yan kasar Turkiyya mazauna kasashen waje suka fara jefa kuri’a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki, idanuwa sun koma kan masu jefa kuri’a na cikin gida wanda su ne za su yanke hukunci na karshe a lamarin dimokradiyyar kasar.

Tsawon shekaru, Turkiyya na samun yaiwatar fitar masu jefa kuri’a a yayin zabuka, inda a zaben 2018 kaso 86 na masu kada kuri’a suka fita rumfunan zabe.

A lokacin da ‘yan kasar Turkiyya da ke kasashen waje za su jefa kuri’unsu a tsakanin 27 ga Afrilu da 9 ga Mayu, za a gudanar da zabe a cikin gida a ranar 14 ga Mayu.

Turkiyya ta samu muhimman sauye-sauye a tsarin gudanar da zabuka tun daga 1990 da suka hada da; fara zaben shugaban kasa kai tsaye a 2014 da kuka sauya tsarin shugabanci zuwa na shugaban kasa a 2017, da kuma samar da sabuwar dokar zabe da ta rage kason kuri’u da ‘yan jam’iyya za ta samu kafin ta shiga majalisa zuwa kaso 7 cikin dari.

Fitar masu jefa kuri’a rumfunan zabe

Tun shekarar 1990 ake samun fitar farin dago zuwa rumfunan zabe a Turkiyya, wanda kaso matsakaici shi ne 78.5. kamar yadda Ma’ajiyar Bayanan Masu Fita Jefa Kuri’a ta IDEA ta bayyana.

Daya daga cikin lokutan da aka samu mafi yawan fitar masu jefa kuri’a a Turkiyya shi ne a lokacin zaben shugaban kasa na 2018, inda kaso 86,2 na masu kada kuri’a suka yi zabe.

A shekarar 2014 ne aka samu mafi karancin fitar masu jefa kuri’a zuwa rumfunan zabe wanda ya kama kaso 74 na adadin wadanda suka cancanci yin zabe.

Kiyasi da dimukradiyyar wasu kasashe

Turkiyya na da yawan fitar masu jefa kuri’a idan aka yi duba ga wasu kasashen duniya --- Girka a 2019, Amurka a 2020, Ingila a 2019, Norway 2021 da Indiya a 2019 duk na kasa da Turkiyya wajen fitar masu jefa kuri’a rumfunan zabe.

Norway ce ta biyu da kaso 77 na masu jefa kuri’a a zaben 2021. Amurka na da kaso 70.7 a zaben shugaban kasa na 2020. Ingila kuma na da kaso 67.5 a zaben 2019.

Girka ce ta samu mafi karanci a tsakanin wadannan kasashe da kaso 57.8 a zaben 2019 yayin da Indiya ta samu kaso 67 a zaben da aka gudanar a 2019 a kasar.