Hukumar Cigaba ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) na gudanar da shirin tara dala miliyan 550 don gudanar da ayyuka 31 da nufin farfado da yankunan da girgizar kasa ta illata a kudancin Türkiye.
Hukumar na kira ga kasashe da Kungiyoyin Kasa da Kasa kan su taimaki gwamnati da jama’ar Türkiye.
Wannan kira na UNDP ya zo ne bayan wani babban taron tallafi na kasa da kasa da aka gudanar a Brussels a ranar 20 ga Maris wanda ya nemi a tattara dala biliyan 7.5 don farfado da yankin kudancin Türkiye da girgizar kasa ta illata.
Taron ya gabatar da bayanai da alkaluman sakamakon binciken da Kwamitin Farfadowa Daga illar Girgizar Kasa da Sake Gina Kasa a Türkiye (TERRA), wanda nazari ne kan kudaden da ake bukata wanda UNDP da Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Turai da Bankin Duniya suka dauki nauyin gudanarwa.
Bayanan na TERRA sun bayyana cewar girgizar kasar ta janyo asarar dala biliyan 103.6.
Sakamakon binciken na TERRA ya bayyana yadda UNDP suka shirya gudanar da aiyuka 31 don sake gina yankunan da suka rushe.
Hukumar na bukatar dala miliyan 550 don gudanar da wadannan aiyuka masu dorewa.
UNDP ta bayyana cewa tagwayen girgizar kasar da suka afku a ranar 6 ga Fabrairu a kudancin Türkiye sun shafi yanki mai girman murabba’in kilomita 110,000. Tare da yin ajalin sama da mutum 50,000.
Haka zalika girgizar kasar ta raba mutum miliyan 3.3 da matsugunansu.
Wakiliyar UNDP a Türkiye Louisa Vinton, ta fada wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa “Girman rusau din da aka samu abu ne da ba a taba tsammani ba”.
Ta kara da cewa, dalilin hakan ya sanya suke bukatar taimako daga kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa.