Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya isa Nakhchivan don tattaunawa da takwaransa na Azabaijan Ilham Aliyev. / Hoto: AA

Shugaban Kasar Azabaijan Ilham Aliyev ya yaba da jawabin da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi a wajen Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya saboda yadda ya dace da dokokin kasa da kasa, da kuma adalci don kare manufofin Azabaijan.

Karabakh yankin kasar Azabaijan ne kuma ba za a taba amincewa da duk wani kaka-gida ko sabon matsayi da za a kawo a yankin ba, in ji Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wajen Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 a New York.

Erdogan ya ce "Tun da fari mun goyi bayan tattaunawar sulhu tsakanin Azabaijan da Armeniya. Sai dai kuma, mun ga yadda Armeniya ba ta yi amfani da wannan dama ta tarihi ba".

A ranar Litinin din nan ne Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya isa yankin Nakhchivan mai cin gashin kansa bayan gayyatar da takwaransa na Azabaijan Ilham Aliyev ya yi masa.

"Alakar Turkiyya da Azabaijan ta musamman ce" in ji Erdogan, inda ya yi alkawarin Ankara za ta ci gaba kokarin hadin kai da Baku.

Shugaba Erdogan ya kara da cewa batu ne na alfahari ga Turkiyya cewa Azabaijan ta samu nasarar yakar 'yan ta'adda a Karabakh, kuma ba tare da illata fararen-hula ba.

A makon jiya, Azabaijan ta kaddamar da "matakan yaki da ta'addanci" a Karabakh da manufar tabbatar da aiki da yarjejeniyar zaman lafiya ta watan Nuwamban 2020 da bangarori uku -- ita da Rasha da Armeniya -- suka cimma bayan kwanaki 44 da suka yi suna arangama da Yerevan.

Tare da nasarar baya-bayan nan da Azabaijan ta samu, an bude sabbin kofofin damarmaki don sasantawar gaba daya a yankin, in ji Shugaba Erdogan.

"Azabaijan da Turkiyya na son zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, ba yaki suke so ba," in ji shugaban Azabaijan Aliyev.

Tun shekarar 1991 rikici ya yi kamari tsakanin Azabaijan da Armeniya a yayin da sojojin Armeniya suka mamaye Karabakh, yankin da a dokar kasa da kasa na Azabaijan ne, tare da wasu yankuna bakawai da ke kusa da wajen.

Erdogan ya ce "Muna sa ran Armeniya ta dauki matakan da suka kai har zuci don zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin,"

Layin bututun iskar gas na Igdir-Nakhchivan

Ankara da Baku a 2020 sun amince da wata yarjejeniya don jigilar iskar gas daga Turkiyya zuwa yankin Nakhchivan na Azabaijan.

Layin bututun iskar gas na Igdir-Nakhchivan zai zurfafa alakar Turkiyya da Azbaijan, kuma zai bayar da gudunmowa wajen aikawa da makamashi zuwa Turai, in ji Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

Layin bututun man mai tsayin kilomita 85 zai tashi daga lardin gabashin Turkiyya na Igdir zuwa Sederek da ke yammacin Azabaijan, inda a kowace shekara zai kai cubicmeter miliyan 500 na iskar gas zuwa yankin.

Za a tabbatar da aikin ta hanyar hadin kai da kamfanin man fetur da iskar gas na Turkiyya BOTAS da kamfanin mai na Azabaijan SOCAR.

A 2021, Turkiyya da Azabaijan sun sanya hannu kan 'Yarjejeniyar Susha", yarjejeniyar da ta mayar da hankali kan hadin kan tsaro da samar da sabbin hanyoyin sufuri.

"Yarjejeniyar Susha ta daga martabar dangantakar Turkiyya da Azabaijan zuwa wani sabon mataki," in ji shugaban Azabaijan Aliyev, inda ya kara da cewa "alakar ta kai kololuwa."

TRT World