Yarjejeniyar safarar hatsi ta Bahar Maliya da Turkiyya ta jagoranta ta kubutar da duniya daga fada wa rikicin abinci/ Hoto AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Rasha ta amince da kara wa’adin yarjejeniyar da ta bayar da dama ga Yukren ta fitar da hatsin da take da shi ta Bahar Maliya.

Ana sa ran hakan zai saukaka hana afkuwar rikicin abinci a duniya saboda yakin Rasha da Yukren da aka fara sama da shekara daya da ta wuce.

Erdogan ya ce ”Tare da kokarin kasarmu, da goyon bayan abokanmu na Rasha da kuma gudunmowar abokanmu na Yukren, an dauki matakin kara wa’adin yarjejeniyar hatsi ta Bahar Maliya na tsawon wata biyu.”

Ya bayar da wannan sanarwa a lokacin da yake bayani ga shuganannin larduna na Jam’iyyar AK, kwana guda kafin ranar 18 ga Mayu da yarjejeniyar farko za ta kare.

Erdogan ya kuma ce “Muna fatan za mu ga kwanakin da za a kawo karshen yakin Rasha da Yukren, za a fara da tsagaita wuta sannan zaman lafiya mai dorewa.

Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya da Rasha da Yukren sun fara sanya hannu kan yarjejeniyar a Istanbul a watan Yulin shekarar da ta gabata, inda aka dawo da safarar hatsi daga tashoshin jiragen ruwan Yukren da ke Bahar Maliya wanda aka dakatar bayan fara yakin Rasha da Yukren a watan Fabrairun 2022.

Yukren da Rasha, manyan kasashe ne da ke fitar da alkama da man girki da sauran kayan abinci masu rahusa zuwa kasashe masu tasowa.

An kafa kwamitin kasashen uku tare da wakilan MDD don sanya idanu kan safarar jiragen ruwan a Istanbul.

Tun daga watan Agustan bara zuwa yau, an fitar da hatsi sama da yawan tan miliyan 30 daga Yukren, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

A yayin bayanin nasa na ranar Laraba, shugaban na Turkiyya ya gode wa takwarorinsa na Rasha da Yukren da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, bisa kokarinsu na ganin an tsawaita wa’adin yarjejeniyar.

Ya kara da cewa “Haka kuma, abokanmu na Rasha sun bayyana cewa ba za su hana jiragen ruwan Turkiyya wucewa daga tashoshin Mykolaiv da Olvia ba. Muna godiya gare su saboda wannan yakana.”

Ministan kayan more rayuwa na Yukren Oleksandr Kubrakov ya gode wa Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya saboda kara wa’adin yarjejeniyar, kuma Kiev na godiya da yaba wa kawayenta bisa kokarinsu na karfafa yadda za a wadata da abinci a duniya.

"An kawar da matsalar hana safarar hatsi ta Bahar Maliya, kuma ana ci gaba da safarar hatsin da sassan duniya”, in ji Kubrakov a wani sako da ya fitar ta shafin Twitter.

TRT World