An ware Gidan Tarihi na Srebrenica-Potocari da makabarta da aka binne wadanda aka kashe a 1995 a yankin Potocari na Srebrenica. / Hoto: AA

Cibiyar Tahiri ta Srebrenica ta kusan cika da "karafa da suka yi tsatsa" idan ba don gudunmawar da Turkiyya ta kai mata ba, in ji daraktanta.

"Ina so na sanar da jama'a abin da Turkiyya ta yi wa cibiyar tarihi ta Srebrenica. Idan ba don Turkiyya da gwamnatin kasar ba, da karafa masu tsatsa ne za su cika ko ina a cikin cibiyar," a cewar Sarki Suljagic, wanda ya tattara tarihin baka daga wadanda suka tsira daga kisan kare-dangi da aka yi a garin Srebrenica na Bosnia da Herzegovina mai cike da tarihi ga gidan talabijin na Hayat TV da ke Bosnia.

“Ba mu da rufi, ba mu da katanga, komai ya ruguje. Hukumar Hadin Kan Turkiyya (TIKA) ta kawo mana mafita. Abin alfahari ne yin aiki tare da abokanmu da ’yan’uwanmu daga Turkiyya,'' in ji shi.

Gidan tarihi na ‘Srebrenica-Potocari Memorial’ da makabarta da aka binne wadanda aka yi wa kisan kare-dangi na 1995 na yankin Potocari na Srebrenica ne.

An ware wajen ne don karrama wadanda aka yi wa kisan kare-dangi na Srebrenica a shekarar 1995, inda ran ‘yan Bosnia Musulmai maza manya da kanana yara sama da 8,000 suka salwanta a garin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana yankin a matsayin wuri da ake “ tsare shi”.

Kisan kare dangi na Srebrenica

Dubban Musulmai maza da yara kanana ne aka kashe bayan harin da dakarun Serb suka kai "yankin da ke da tsaro" na Majalisar Dinkin Duniya a Srebrenica a watan Yulin 1995, duk da kasancewar sojojin Holland da ke aiki a matsayin dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa a wajen.

Dakarun Sabiya sun yi wa Srebrenica kawanya, a kokarin da suka yi wajen kwace yankin daga hannun Musulmai ‘yan Bosniya da Croat don kafa wata kasa.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ayyana Srebrenica a matsayin wurin da "yake da tsaro" a lokacin bazara ta shekara ta 1993.

Amma sojojin Sabiya karkashin jagorancin Janar Ratko Mladic, wadanda daga baya aka same su da laifukan yaki da cin zarafin bil'adama da kisan kare-dangi, sun mamaye yankin na MDD.

Dakarun Holland sun gaza yin aikinsu yadda ya kamata sakamokon mamaye yankin da dakarun Sabiya suka yi, inda a ranar 11 ga watan Yuli suka kashe maza da yara maza 2,000.

Kimanin 'yan Bosniya 15,000 ne suka gudu zuwa tsaunukan da ke kewaye da su, amma sojojin Sabiyawa suka yi farautarsu suka kashe mutane 6,000 a cikin dazuzzuka.

TRT World