Girgizar kasa ya afku a yankin Malatya ta sanya ta mazauna wuraren fitowa kan tituna. / Hoto: AA

An fuskanci girgizar kasa mai karfin maki 5.3 a gundumar Yesilyurt da ke Malatya a kasar Turkiyya, a cewar hukumar kula da takaita aukuwar bala'o'i ta kasar, AFAD.

Girgizar kasar ta ranar Alhamis ta faru ne da misalin karfe 8:48 na dare a agogon kasar kuma an ji ta ne daga lardunan da ke makwabtaka da Kahramanmaras da Adiyaman da Sanliurfa da kuma Gaziantep.

An dai ga mazauna yankin suna ta kokarin neman hanyar tsira da kare kansu daga rushewar gine-gine.

Mutane 23 ne suka jikkata sakamakon firgici da kokarin neman tsira, sai dai ba a samu wani rahoto na mutuwar mutane ba kawo yanzu, a cewar ministan lafiya Fahrettin Koca.

Fahrettin ya ce an aike da motocin daukar marasa lafiya 14 da kuma kungiyoyin agaji uku na UMKE zuwa yankin da abin ya shafa domin kai agaji.

Kazalika Ministan harkokin cikin gida na Turkiyyar Ali Yerlikaya ya ce dukkan hukumomin gwamnatin kasar musamman AFAD sun fara gudanar da bincike a yankin.

A nasa bangaren, Ministan Muhalli da Birane Mehmet Ozhaseki, ya ce tawagoginsa sun isa lardunan inda suke aikin tantance barnar da aka samu.

Zurfin girgizar kasar da ta auku ya kai nisan kilomita bakwai, a cewar hukumomi.

Sabuwar girgizar kasar ta haifar da firgici ga mazauna yankin wadanda suka taba fuskantar munanan girgizar kasa sau biyu a watan Fabrairun shekarar nan.

Sama da mutane 50,000 ne suka mutu a Turkiyya sakamakon tagwayen girgizar kasa da aka yi a kudancin lardin Kahramanmaras ranar 6 ga watan Fabrairu, kuma mutane miliyan 13 a larduna 11 lamarin ya shafa.

TRT World