Ministan harkokin waje na Turkiyya Hakan Fidan zai gana da ministan harkokin waje na Ukraine Andriy Sibiha ranar 21 ga Oktoba, wadda za ta zama ziyarar Sibiha ta farko zuwa Turkiyya. Zantawarsu za ta nuna goyon bayan Turkiyya kan 'yancin ƙasar Ukraine, da neman warware yaƙi ta diflomasiyya, da inganta dangantaka.
Ziyarar na zuwa ne bayan wadda Fidan ya kai a watan Agusta zuwa Ukraine, inda ƙasashen biyu suka nemi inganta alaƙa, musamman a tattalin arziƙi, da makamashi, da ɓangaren tsaro. Ana sa ran sanya hannu kan takardar fahimtar juna da na tuntuɓa don 2025-2026.
Tun lokacin da Turkiyya da Ukraine suka ɗaga darajar alƙarsu zuwa ta musamman a 2011, an samu babban cigaba a ɓangarori da dama, inda tsaro da makamashi suke kangaba.
Minista Fidan ya haɗa da Sibiha a Oktoban 2024 yayin taron ƙoli na Ukraine da gabashin Turai a Dubrovnik. Yayin da yaƙi ke ci gaba, an tattauna kan tsaro a yankin.
Taron mia zuwa ana sa ran zai ƙarfafa matsayin Turkiyya a matsayin mai shiga tsakani, mai goyon bayan warware rikici ta amfani da dokoki duniya.
Haɗin kan tattalin arziƙi da cinikayya mara shinge
Alaƙar tattalin arziƙi tsakanin Turkiyya da Ukraine ta haɓaka sosai, duka da ana rikici. A 2023, kasuwanci tsakaninsu ya kai dala biliyan $7.3.
Tattaunawa yayin ziyarar za ta mayar da hankali kan yarjejeniyar cinikayya mara shinge tsakanin ƙasashen biyu, wadda ake sa ran za ta fara aiki ba jimawa.
Yarjejeniyar ana kallonta a matsayin babban mataki na haɓaka kasuwanci tsakaninsu a tsawon lokaci.
Turkiyya ta taka rawa mai muhimmanci wajen aiwatar da ayyukan diflomasiyya da na jin-ƙai yayin yaƙin. A 2022, ta karɓi baƙuncin taro na farko tsakanin wakilan Ukraine da Rasha.
Bugu da ƙari, ƙoƙarin Turkiyya na shirin fita da hatsi ta Bahar Aswad, wanda ya ba da damar fita da tan miliyan 33 na hatsin Ukraine, ya zamo babban abin da ya rage haɗarin yunwa a duniya.
Sannan Turkiyya ta shiga shirin musayar fursunoni tsakanin Ukraine da Rasha, wanna ya ƙara nuna matsayarta wajen kawo zaman lafiya a yankin.
Ziayarar ana sa ran za ta ƙarfafa aniyar Turkiyya kan dangantaka da ɗorewar zaman lafiya a yankin da ci gaba da zama babbar mai taka rawa wajen sulhu da goyon bayan Ukraine.