Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa yana sa ran bangarorin da suka kulla yarjejeniyar fitar da hatsi ta Tekun Bahar Rum wadda za ta kawo karshe a ranar Litinin za su kara tsawaita t.
“Muna shirin karbar (Shugaban Rasha Vladimir) Putin a Turkiyya a watan Agusta. Muna goyon bayan kara tsawaita yarjejeniyar fitar da hatsi ta Bahar Rum.”
“(Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio) Guterres ya tura wasika ga Putin. Muna sa ran da wannan takarda, za mu samu tabbacin kara tsawaita yarjejeniyar fitar da hatsi da taimakonmu da na Rasha,” kamar yadda Shugaba Erdogan ya shaida wa manema labarai bayan Sallar Juma’a a Santambul.
Wannan zai taimaka wurin shawo kan matsalolin da kasashen Afirka da ke cikin talauci ke fuskanta, kamar yadda Shugaba Erdogan ya bayyana inda ya kara da cewa shi ma Shugaba Putin ya amince da hakan.
A baya, Putin ya yi yunkurin tura hatsi ga matalautan kasashe a kyauta.
A shekarar da ta gabata, Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya da Ukraine sun saka hannu kan wata yarjejeniya a Istanbul domin ci gaba da fitar da hatsi daga tashoshin ruwa na Tekun Bahar Rum uku wadanda aka dakatar da jigilar hatsi daga gare su bayan an soma yakin Rasha da Ukraine a Fabrairun 2022.
An samar da wata cibiya ta hadin gwiwa a Istanbul wadda ta kunshi jami’ai daga kasashen uku da kuma Majalisar Dinkin Duniya domin sa ido kan jigilar hatsin.
Jirgi na farko wanda ke dauke da hatsin a karkashin yarjejeniyar mai cike da tarihi ya bar tashar ruwa ta Odesa da ke Ukraine a watan Agusta.
Kasashen duniya sun jinjina wa Turkiyya kan irin rawar da ta taka wurin shiga tsakanin Ukraine da Rasha, inda kuma kasar ta sha kira kan Kiev da Moscow da su kawo karshen rikicin da suke yi ta hanyar sasanci.
Sai dai jami’an Rasha sun soma tsegumta cewa akwai bukatar a wannan watan su dakile yunkurin sabunta yarjejeniyar fitar da hatsin, inda suke kokawa kan cewa ba a cika wasu alkawura na yarjejeniyar ba ta bangaren fitar da kaya daga Rasha.
Kawance da kasar Girka
Idan aka koma ta bagaren kawance da kasar Girka, Shugaba Erdogan ya kara jaddada cewa shi da Firaiministan Girka Kyriakos Mitsotakis duka shugabanni ne wadanda aka sake zabarsu, kuma suna da buri iri daya na bin “madaidaiciyar hanya.”
Erdogan da Mitsotakis sun hadu a ranar Laraba a lokacin taron kungiyar NATO a Vilnius babban birnin Lithuania. Abubuwa mafi muhimmanci da Erdogan ya ce ya tattauna da Mitsotakis suna da alaka da “Yammacin Yankin Thrace, kan batun Mufti.”
Yammacin yankin Thrace na Girka kusa da iyakar Turkiyya na da Musulman Turkiyya akalla 150,000 wadanda suka dade a wurin.
Turkawa na da ‘yanci a wurin tun bayan yarjejeniyar Lausanne da aka cimmawa a 1923, sai dai lamarin ya kara lalacewa a shekarun baya, inda kasar Girka ta ki amincewa da wasu malaman addini wadanda Musulman suka zaba.
Erdogan ya alamta cewa akwai yiwuwar ya hadu da Mitsotakis a nan gaba bayan shirye-shirye na wucin gadi da jakadu da ministocin harkokin kasashen waje na kasashen biyu suka yi.
Shirin Turkiyya na shiga Tarayyar Turai
A lokacin da yake tattaunawa da sauran shugabanni a Vilnius, Erdogan ya ce ya tattauna kan batun Turkiyya ta zama mamba a Tarayyar Turai.
“Mun tattauna dalla-dalla da shugabannin kasashen Tarayyar Turai kuma na shaida musu, ‘Muna son a dauki matakai masu kyau kan Turkiyya, wadanda EU din ta ki dauka tsawon shekaru 52.’,” kamar yadda ya kara da cewa.
Turkiyya ta rubuta bukatar zama mamba a kungiyar EU tun a 1987, sa’annan kuma ta zama kasa mai jiran zama mamba tun a 1999.
An soma tattaunawa domin zama cikakkiyar mamba tun a Oktobar 2005 sai dai an ta jinkirtar da lamarin a tsawon shekaru sakamakon siyasa da wasu kasashe suka kawo cikin lamarin.