Turkiyya za ta gaya wa kasashe mambobin OIC hanyoyinta na hana nuna kyama ga Musulunci. / Hoto: AFP

Turkiyya za ta dauki tsattsauran mataki sannan ta sanya ido sosai kan kasashen da ake nuna kyama da kiyayya ga Musulunci, a cewar wasu majiyoyin diflomasiyya na Turkiyya a wata sanarwa.

An fitar da sanarwar ce a yayin da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya halarci taron da aka yi ranar Litinin ta manhajar bidiyo na kungiyar Hada Kan Kasashen Musulmai ta Organisation of Islamic Cooperation (OIC).

“Turkiyya za ta fadi ra'ayinta game da wannan batu ga kasashe mambobin OIC da ke kuma kungiyoyi irin su OSCE (Kungiyar Tsaro da Hadin Kan Turai, da Kungiyar 'Yan Majalisar Dokokin Turai da kuma Hukumar Tarayyar Turai cewa ba ta goyon bayan nuna wariya da kyama,” in ji sanarwar.

Kazalika kungiyar ta OIC ta yaba wa matakin kasar Kuwait na fassara Alkur'ani zuwa harshen Sweden da kuma raba kwafi 100,000.

"Muna kira ga mambobinmu su jaddada rashin amincewarsu ga kona Alkur'ani a wadancan kasashe, sannan su sake nazari kan dangantakarsu ta siyasa da tattalin arziki da al'ada da wadannan kasashe,” a cewar sanarwar.

Hana kyamar Musulunci

Kungiyar ta nemi a samar da wani wakili na musamman da zai yi aiki tukuru wajen ganin an daina kyamar Musulunci wanda za a ba shi damar yin amfani da kowace hanya ta kungiyar.

Kasashe mambobin OIC sun mika bukata ga Majalisar Dinkin Duniya domin ta nada wakili na musaman da zai hana nuna kyama ga Musulunci.

A yayin taron ta manhajar bidiyo, ministocin harkokin wajen kasashe da dama sun jaddada muhimmancin tuntubar Kasashen Yamma da hukumomin duniya domin su sanya ido sosai kan masu kona Alkur'ani musamman a Turai.

AA