Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta bayyana cewa, Turkiyya za ta ci gaba da nuna adawa da kisan kiyashin da ake yi a Gaza tare da goyon bayan tabbatar da adalci ga al'ummar Palasdinu. / Hoto: AA  

Turkiyya ta yi watsi da "kalaman batanci" da Firaministan Ministan Isra'ila ya yi wa Shugaba Recep Tayyip Erdogan, tana mai cewa jami'an Isra'ila ba su da "ikon magana kan doka."

Jami'an Isra'ila, wadanda suka shiga cikin bakin tarihi da zalunci da kuma kisan kiyashi da ake yi wa al'ummar Falasdinu, ba su da hurumin yin magana kan wata doka," a cewar Ma'aikatar Harkokin wajen Isra'ila a ranar Laraba.

"Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Ministan Harkokin Wajen kasar Eli Cohen, wadanda dukkansu ba su ji dadin gaskiyar da ake bayyana wa duniya ba, ba za su iya boye laifukan da suka aikata ba tare da batancinsu mara tushe kan Recep Tayyip Erdogan kuma shugaban Jamhuriyar Turkiyya ba," in ji Ma'aikatar.

Ma'aikatar ta jaddada cewa, ''Wadanda suka ta da husuma da kuma aikata laifukan cin zarafin bil'adama, da suka haifar da tashin hankali da janyo Allah wadai daga al'ummar duniya, ko mu jima ko mu dade za su fuskanci shari'a.''

"Mahukuntan Isra'ila, wadanda tuni suka rasa kimarsu ta jinkan dan adam, ba za su iya boye irin laifukan da suka aikata ta hanyar jefa bama-bamai a asibitoci da kuma kashe mata da yara a idon duniya ba kuma a yanzu ba za su iya karkatar da hankali kowa zuwa gare su," in ji Ma'aikatar.

Turkiyya za ta ci gaba da tsayawa tare da nuna adawa da kisan kiyashin da ake yi a zirin Gaza na Falasdinu da kuma ba da goyon bayanta wajen tabbatar da adalci ga al'ummar Palasdinu baki daya, a cewar Ma'aikatar harkokin wajen kasar.

TRT World