Ankara ta jaddada muhimancin rawar da UNIFL ke takawa wajen samar da tsaro a yankin bayan hare-hare munana da Isra'ila ta kai Lebanon. / Photo: AA Archive

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta soki harin da Isra'ila ta kai wa Dakarun Majalisar Ɗinkin DUniya na Wucin-Gadi a Lebanon (UNIFIL), inda ta yi gargaɗi kan mamayar Isra'ila zuwa Lebanon.

A wata sanarwa, Ma'aikatar ta jaddada muhimancin rawar da UNIFL ke takawa wajen samar da tsaro a yankin bayan hare-hare munana da Isra'ila ta kai Lebanon.

"An kai Dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya na Wucin-Gadi a Lebanon (UNIFIL) don bayar da gudunmawa wajen samar da tsaro a yankin. Rawar da UNIFL ke takawa ta fi muhimmanci, idan aka kalli yadda Isra'ila ke da manufar yada yaƙi a dukkan yankin."

Ma'aikatar ta kuma ce "Yawaitar hare-haren Isra'ila kan dakarun UNIFL shaida ce ta manufofin Netanyahu na mamayar Lebanon, da kuma shirinta na amfani da makamai a kowane yanayi."

Gwamnatin Ankara ta yi kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki matakan ƙalubalantar Isra'ila da dukkan ƙasashen da suke ba ta makamai.

"Kowane mamba a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya na da alhakin dakatar da hare-haren Isra'ila a kan dakarun MDD da su da kansu suka tura su aiki."

Harin Isra'ila kan UNIFIL

A ranar Lahadi, dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a Lebanon sun ce tankokin yaƙi na Isra'ila sun kutsa kai ta cikin wata ƙofa tare da shiga iyakar Lebanon, bayan sun hana su motsawa kwana guda kafin wannan rana.

Lamarin na zuwa ne bayan Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi kira ga Shugaban MDD da ya janye masu wanzar da zaman lafiyar da ke kudancin Lebanon, yana mai cewa Hezbollah na amfani da su a matsayin mafaka.

Dakarun na UNIFL sun ƙi barin wajen da suke a kudancin Lebanon.

TRT World