Turkiyya na bukatar a kyale masana tarihi su bayyana me ya faru a 1915/ Hoto: TRT World

Turkiyya ta soki Shugaban Kasar Amurka Joe Biden bisa kalaman da ya yi kan abubuwan da suka faru a shekarar 1915 tsakanin Turkiyya da Armeniya.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya fitar da wani sako ta shafinsa na Twitter cewa, “’yan bangar siyasa sun sake yunkurin jirkita tarihi.

"Kalaman da aka yi da manufa ta siyasa ba za su taba sauya gaskiya ba. Dole ne a dinga tunawa da mutanen da suke dagewa kan kura-kuransu da sunan munafukai. Kar wanda ya yi garajen koya mana tarihinmu.”

A gefe guda kuma Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi watsi da kalamai da abubuwan da shugabannin wasu kasashen waje ke fada, inda ta ce Ankara ta dauke su “marasa tasiri”, kuma tana la’antar duk wanda “ya ci gaba da zama a kan wannan kuskuren”.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta kara da cewa “kalamai marasa dadi da kyau da suka ci karo da gaskiyar tarihi da dokokin kasa da kasa game da abubuwan da suka faru a 1915, na da manufar sake rubuta tarihi don biyan bukata a siyasance, Turkiyya ba ta bukatar a koya mata tarihinta.”

Sanarwar ta kara da cewa "'yan siyasa ba su da hurumin bayyana me ya faru a 1915 don cimma manufofi da bukatunsu na cikin gida.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa “Wannan mataki zai jirkita tarihi ne kawai. Wadanda suke nacewa kan wannan ra’ayi za su wulakanta a tarihi, su kuma kare a matsayin ‘yan siyasa marasa daraja.”

‘Cimma burukan siyasa’

Gwamnatin Ankara ta kuma yi kira ga masu son ja wa kansu tsana da kiyayya daga tarihi don biyan bukatunsu na siyasa, da su dawo daga rakiyar ‘babban kuskure’ su mara wa kwamitin masana tarihi na hadin gwiwa da Turkiyya ke jagoranta baya.

Matsayin Turkiyya game da abubuwan da suka faru a 1915 shi ne mutuwar Armeniyawa a gabashin Anatoliya da ta afku sakamakon yadda wasun su suka hada kai da bangaren Rasha tare da bijire wa Daular Usmaniyya.

Kokarin sauya wa Armeniyawa waje ne ya janyo asarar rayuka da dama.

Turkiyya ta kalubalanci bayyana lamarin na 1915 a matsayin ‘Kisan Kare Dangi’ inda ta bayyana shi a matsayin balahirar da ta shafi dukkan bangarori.

Turkiyya ta sha bayar da shawarar a kafa kwamitin hadin gwiwa na masana tarihi daga Turkiyya da Armeniya da kuma masana na kasa da kasa don tattauna wannan batu.

TRT World