Wakilin Turkiyya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Sedat Onal, ya bayyana bukatar sake fasalin Kwamitin Tsaro na Majalisar ta yadda za a magance kalubalen da yake fuskanta a yanzu.
"Ba za a iya kawar da bukatar yin garambawul a kwamitin tsaron ba," a cewar Onal a ranar Talata yayin muhawara a zauren MDD kan sake fasalin kwamitin tsaron majalisar.
"Abubuwan da suka faru a 'yan kwanakin nan a kwamitin sun tabbatar da hakan," in ji shi, yana mai nuni da gazawar majalisar wajen tabbatar da tsagaita da kuma dakatar da wahalhalun da 'yan'adam a Falasdinu ke fuskanta "sakamakon rashin tabuka wani abin a zo a gani'' daga kwamitin.
Onal ya jaddada cewa tsarin garambawul din na bukatar yin nazari tare da kawar da kura-kuran da majalisar ke fuskanta a halin yanzu.
Wakilin ya kara da cewa "Dole ne a daidaita manufofin kwamitin na dimokuradiyya tare da samar da ingantaccen yanayin sadaukarwa ba tare da nuna son rai ba."
"Yin hakan ya kunshi cikakken tsari mai hade da sadaukarwa da zai amfanar tare da samun goyon bayan dukkan kasashe mambobin majalisar, wanda kuma zai jaddada tare da fifita maslaha ta bai-daya fiye da muradun wata kasa," in ji shi.
Tambaya kan hakkokin kwamitin majalisar
A yayin jawabinsa yayin muhawarar, Shugaban zauren Majalisar Dennis Francis ya ce idan ba a gyara tsarin kwamitin ba, ayyukan Majalisar da hakkokinta za su fuskanci tarin matsaloli.
"Tashe-tashen hankula da yake-yake suna ci gaba da yaduwa a yankuna da dama a fadin duniya, yayin da a bangare guda alamu suka yi nuni da cewa akwai rarrabuwar kawuna a kwamitin tsaro na MDD.
Kwamitin dai ya zartas da wani kuduri kan rikicin Falasdinu a ranar Laraba, bayan yunkuri hudu da bai yi nasara ba tun bayan barkewar rikicin a farkon watan Oktoba.
Kasashe da dama mambobin MDD ciki har da Turkiyya suna da yakinin ceewa mafita ita ce a gaggauta yin garambawul a kwamitin tsaron a wannan lokaci.
A wannan yanayin da ake ciki, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sha kira kan a yi irin wannan garambawul ga kwamitin.