Matan shugabannin sun dauki hoto a gaban muhimman kayayyaki, ciki har da "Las Meninas" na Velazquez da "Still Life with Lemons, Oranges da Roce" na Zurbaran." / Hoto: TRT World

Mai dakin shugaban kasar Turkiyya Emine Erdogan ta ziyarci gidan adana kayan tarihi na Prado da ke Madrid, tare da Maria Begona Gomez Fernandaz, matar Firaiministan Spaniya Pedro Sanchez.

A yayin rakiyar shugaban kasar Turkiyya Recep tayyip Erdogan zuwa taron gwamnatocin Turkiyya-Spaniya karo na 8 a birnin Madrid, an zagaya da Emine Erdogan shahararren gidan adana kayan tarihi na Prado tare da matar Firaiministan Spaniya.

Gidan adana kayan tarihin da tattara kayan masarautu, na gabatar da kayan sharararrun masu zane 'yan Spaniya irin su El Greco, Diego Velazquez, Francisco de Zurbaran da Goya, da kuma masu zane na Holland irin su Bosch da Rubens.

Fernandez ta yi wa matar Erdogan cikakkun bayanai game da kayayyakin.

Matan shugabannin sun dauki hoto a gaban muhimman kayayyaki, ciki har da "Las Meninas" na Velazquez da "Still Life with Lemons, Oranges da Roce" na Zurbaran.

A yayin zaga gidan adana kayan tarihin, sun gana da dalibai da daukar hotuna tare. Bayan zagayen, Erdogan da Fernandaz sun ci abincin rana.

Emine Erdogan ta bayyana yadda ta ji a yayin ziyarar ta shafinta na sada zumunta da cewa:

"Mun ziyarci daya daga gidajen tarihi mafi tsufa a kasar, gidan adana kayan tarihi na Prado, a yayin halartar Taron Gwamnatocin Turkiyya-Spaniya karo na 8 a Madrid.

"Mun yi duba na tsanaki ga kayayyakin zane-zane da sassake-sassake tun daga na karni na 12 zuwa karni na 19, da ma kayan tarihin sarakunan Spaniya.

"Kowanne abu a gidan adana kayan tarihin na bayyana wani bangare na Spaniya. Ina godiya ga Miss Fernandaz saboda karramawar da ta yi mana."

TRT World