An dauki matakin a wajen taron Kwamitin Kayan Tarihi na Duniya na UNESCO da aka yi a birnin Riyadh na Saudiyya. Hoto: AA

An saka tsohon garin Gordion, babban birnin sakafar Phyrgiyawa na Turkiyya, a cikin jerin sunayen wuraren tarihi na UNESCO, in ji Ministan Raya Al'adu da Yawon Bude Ido na Turkiyya.

A wani sako da ya fitar ta shafin Twitter a ranar Litinin ya ce "Muna da labari mai kyau! Mun shigar da wuri na 20 a jerin Kayan Tarihi na UNESCO, Tsohon Garin Gordion, daya daga cikin wurare na musamman na al'ada da ke Ankara ya zama "Kadarar Duniya ta Tarihi".

Da yake gode wa wadanda suka bayar da gudunmawa kan nasarar da aka samu, Ersoy ya ce "Ba a gama komai ba! Muna jiran wani sabon labarin mai dadi daga UNESCO."

Ya kara da cewa "Tare da wannan labari mai dadin ji, muna sa ran shigar da Masallatan Anatoliya da aka tokare da katato, muna sa ran kara yawan wuraren tarihi da muke da su a jerin sunayen UNESCO."

Gordion na daya daga cibiyoyin tarihi mafiya muhimmanci a Gabas ta Kusa, kamar yadda UNESCO ta bayyana a shafinta na yanar gizo.

Tsohon garin Gordion nan a nisan kilomita 90 kudu maso-yammacin Ankara, wanda ke tsakanin wuraren da aka kafa manyan dauloli irin su Assyriyawa da Babilawa da Hitit da Rumawa.

Sanarwar ta kara da cewa wajen "Na a waje mai muhimmanci da kusan dukkan wasu fatake ke bi ta garin da ya hada Tekunan Aegea da Bahar Rum, da ma Gabas Ta Kusa."

Shafin yanar gizo ya kuma kara da cewa "Muhimmancin Gordion a tarihi ya samu ne saboda yadda ya wanzu shekaru 4,500 da suka gabata, tun daga zamanin tagulla (Shekaru 2,500 kafin Miladiyya) zuwa zamanin Medieval (Shekaru 1400 Miladiyya), sannan ya kawo har zuwa zamanin yau."

Sanarwar ta ce "Sarki Midas ne ya shugabanci masarautar Phyrigiyawa, wanda aka bayar da labarin tsananin dukiyarsa daga yadda duk abun da ya taba sai ya zama zinare, kuma shekaru da dama bayan rushewar daular, gwagwarmayar Phyrigiyawa ta zama mai alaka ta kusanci ga nasarar Alexandra Mai Girma a karshen karni na hudu kafin Miladiyya."

TRT World