Otal din ya shiga jerin otal din duniya 50 mafiya kasaita. Hoto/Others

Hotel Museum da ke yankin Cappadocia yana daga cikin manyan otel 50 mafi kasaita da alfarma na duniya, kamar yadda wata mujallar Amurka ta Robb Report ta sanar a ranar Litinin.

Otel din, wanda shi kadai ne na kasar Turkiyya da aka sanya a cikin jerin, ya shiga cikin otel mafi kyau a duniya.

An gina otel din a cikin baraguzai da koguna. Otal din na cike da kayayyakin tarihi daga daulolin Roma da Seljuk da Usmaniyya wadanda duka ke da rajista da gidan tarihi na Nevsehir.

Mujallar ta bayyana cewa a cikin dakuna 34 da ke otel din, babu wanda yake kama da wani.

An bude Museum Otel a 2003 wanda yake a Uchisar wanda wuri ne da hukumar UNESCO ta ware a matsayin wurin tarihi a Cappadocia.

“Dakuna mafi girma da kyau har suna da manyan tafkunan wanka a cikinsu,” in ji Jinathan Alder, daya daga cikin wadanda suka shahara a wurin tafiye-tafiye wanda kuma Robb Report din ta amince da shi.

“Abincin safen otel din shi ne mafi dadin da na taba ci a rayuwata, haka kuma na daren yana da dadi sosai da ba za ka yi tunanin wani wuri ba ma. Suna da wuri na musamman na hada lemo, inda hakan yake zama lamari mai dadi,” in ji Alder.

Hawa mai dutse

Tolga Tosun, babban manajan otel din, ya bayyana cewa: “A Museum Otel, abin da muka fi mayar da hakali a kai shi ne yi wa bakinmu.

“Fito da mu a irin wannan jerin suanye mai daraja wata alama ce ta yadda muke aiki tukuru da kokarin da muke yi,” in ji Tosun.

Cappadocia ta yi fice saboda tudu da kwarinta da yanayin yadda gidaje suke na duwatsu.

Yanayin tsaunin wurin ya samu ne tsawon miliyoyin shekaru inda iska da ruwa suke sassake kasan toka da talgen duwatsu masu aman wuta.

AA