Bozdag Film

An bude wa maziyarta dakunan shirya fina-finai na Bozdag, da a cikinsu aka gabatar da mashahuran fina-finai da suka yi nasara irin su ‘Dirilis Ertugtul’, ‘Kurulus Osman’ da ‘Destan’ wanda nan da nan suka zama wajen tururuwar masu kallon fina-finan Turkiyya.

Wajen wanda aka amince da shi, shi ne irin sa na uku mafi girma a duniya kuma na daya a Turai, cibiyoyin shirya fina-finai na Bozdag na ilmantar da maziyarta tare da daukar su zuwa balaguro mai nisa na tarihin Turkiyya, wanda ya fi mayar da hankali ga zamanin Daular Usmaniyya.

A lokacin da cikin nutsuwa kuke taka kafafuwanku don shaida wadannan kasaitattun wurare da aka gina don shirye-shiryen talabijin masu dogon zango, ana tafiyar da kwakwalen maziyarta zuwa wani zamani da ya shude, inda gine-ginen da aka yi suke sake bayyana tsantsar tarihin Turkiyya.

Wajen da aka samar da wadannan cibiyoyi na da bangarori daban-daban, da suka hada da Fadar Inegol da Kasuwar Urgenc da Fadar Marmaracik da Kasuwar Yenisehir (Sabongari) da Fadar Kulucahisar da Fadar Harzemshah da Bangarorin Kabilun Sogut da Kayi.

Kowanne bangare na bayanin wani bangare na musamman na tarihin Daular Usmaniyya, tare da sanya zukatan maziyarta ninkaya a kogin al’adun Turkawa.

A tsakiyar bangaren Kabilar Kayi, wanda aka dinga nuna wa a mashahuran fina-finan ‘Dirilis Ertugrul’ da ‘Kurulus Osman’, ba hotunan tarihin Daular Usmaniyya kawai maziyarta za su gani ba, har ma da yin wasu abubuwa na nishadi.

Zaurukan shirya fina-finai na bozdag na kayatar da masu kallon fina-finan Turkiyya masu dogon zango a dukkan sassan duniya. Photo: AA

Me ake samu da gani a wajen?

Tun daga sukuwar dawaki zuwa shaida yadda ake shirya fina-finan Turkiyya, baki na shaida yadda rayuwar yau da kullum ta Kabilar Kayi take, suna samun cikakkun bayanai game da zamanin da suka rayu.

Amma kuma, kyawun cibiyoyin shirya fina-finan ya fi gaban batun shirya fim kawai. Maziyarta na haduwa tare da gana wa da jaruman da suka fito a shirin fina-finan da aka shirya a wajen don bayyana tarihi kamar a yau.

A dakunan shirya fina-finai na Bozdag aka gabatar da mashahuran fina-finai da suka yi nasara irin su ‘Dirilis Ertugtul’, ‘Kurulus Osman’ da ‘Destan’. Photo AA

Ga wadanda suke son shakatawa da annushuwa mara misaltuwa, bangaren Sogut ne suke shiga. Maziyarta na iya shan gahawa da lemunan gargajiya a lokacin da suke kashe kwarkwatar idanuwansu a wajen.

Dadin dadawa, wani shagon sayar da kayayyaki na bayar da damar mallakar wani abu na tarihin Daular Usmaniyya, akwai tufafin gargajiya na Daular Usmaniyya da ake sayarwa a wajen.

Maziyarta na yi abubuwa da yawa a wajen kuma za su iya sayen tufafin gargajiya na Daular Usmaniyya. Photo: AA

Dakunan shirya fina-finai na Bozdag sun zama wuraren ban sha’awa da ake ziyarta ba ga Turkawa kadai ba, har ma da al’umun kasashen waje musamman daga Gabas ta Tsakiya da Tsakiyar Asiya da Afirka da Balkan da Latin Amurka.

Mafarkin da ya zama gaske

Mehmet Bozdag, shugaban hukumar gudanarwar Kamfanin ‘Bozdag Film’ mai shirya finai-finai, darakta kuma marubucin fim, a lokacin da ya fara jagorantar shirya ‘Dirilis Ertugrul’ ya bayyana irin yadda yake mafarkin ganin an fadada wajen tare da bai wa maziyarta damar kashe kwarkwatar idanuwansu.

Ya bayyana cewa “Irin abubuwan da muka gani masu kama da wadannan a kasashen waje ne suka zaburar da mu, muka ga lallai tarihinmu mai muhimmanci ya cancanci irin wannan waje, kuma masu kallo su zo su gan shi a zahiri.

"A wadannan wurare aka dauki fina-finan, za a ga kyawu da kyalyalin wajen, tare da irin kokarin da aka yi don samar da shi.”

Zaurukan shirya fina-finai na Bozdag na dauke da gine-ginen da ke bayyana tarihin Daular Usmaniyya. Photo AA

Tun bayan fara ayyuka a wajen, dakunan shirya fina-finan sun dinga samun sha’awar ziyarta daga mutane a ciki da wajen Turkiyya, wadanda suka kayatuwa da yadda wajen ya zama sama da dakin shirya fim kawai.

Bozdag ya bayyana godiyarsa da cewa “Gamsuwar masu kallon mu na da muhimmanci. A ko yaushe muna gwagwarmaya don inganta kyawun dakunan shirya fina-finanmu, ta yadda kowanne maziyarci zai tafi da tunanin waje a kwakwalwarsa.”

Da yake hangen gobe, Bozdag ya bayyana shirinsu na shirya manyan taruka a wannan waje.

Tare da ayyuka da abokansa, ya yi hasashen sake samun masu kallo da za su wajen su akalla dubu talatin ko dubu arba’in daga watan Afrilun shekara mai zuwa.

TRT World