TOMTAS, kamfanin kera jiragen sama na farko a Turkiyya, na da tarihi game da yadda aka dinga rufe shi da yi masa suaye-sauye, wanda tarihinsa ke koma wa ga shekarun 1920.
Sauyin shugabanci a tsakanin yakin duniya har guda biyu ne ya yi tasiri kan kafawa da kulle kamfanin.
Tare da hadin kai da wani kamfanin kasar Jamus, kamfanin samar da jiragen ya fuskanci gogayyar Jamus da Faransa.
A lokacin da Amurka ta matsa lamba kan Babban Tallafin 1950, kamfanin kera jirage na Turkiyya ya zama mai jigilar kayayyaki da kuma zama wajen gyara kayan Ma'aikatar Tsaron Turkiyya.
Kamfanin da matsin lambar bangarorin duniya biyu suka sanya aka rufe tsawon shekara 70, a yanzu ya dawo hayyacinsa, madalla ga manufar ganin Turkiyya ta tsaya da kafarta.
Amma kuma TOMTAS na wakiltar wani zamani na tarihi da aka yi shi cikin wahalhalu na yakin duniya na I da na II. Sake bude shi wani bangare ne na habaka cikin sauri da kasar ke yi.
Duba ga tarihin kamfanin
Bayan kafa Kungiyar Ma'aikatan Jiragen Sama ta Turkiyya a 1925, sai aka samar da kamfanin tare da hadin gwiwar wani kamfanin jamus mai suna Junkers. An bude kamfanin a hukumance a ranar 6 ga Oktoba 1926 a lardin kayseri na Turkiyya.
An baiwa kamfanin sunan "Kamfanin Tayyare (Jirgin sama) da Injin Turkiyya. (TOMTAS)”
Amma kuma, wannan hadin gwiwa tsakanin Jamus da Turkiyya bai yi tsawon rai ba, inda ya kawo karshe a 1928 saboda gazawar kamfanin na Jamus wajen cika ka'idojin yarjejeniyar da aka kulla kan magance bambancin albashi tsakanin ma'aikata Jamusawa da Turkawa.
A ranar 27 ga Oktoba 1928, aka sanar da kamfanin ya durkushe gaba daya.
A wancan lokacin, akwai matsin lamba daga Faransa kan kamfanin na Jamus saboda Faransa na sayar da jiragen sama ga Rundunar Sojin Saman Turkiyya .
Bayan wannan karaya ta kamfanin, an sake bude shi a 1931 da sabon sunan Masana'antar Kera Jiragen Sama ta Kayseri.
A lokacin da yake aiki, dukkan jiragen da ake samarwa a kamfanin sun samu ne daga kamfanonin kasashen waje bisa yarjejeniyar da aka kulla da su kamar irin su Jenkers, The Curtiss Aeroplane da kuma Kamfanin Motor Inc., ga irin su Gothaer Waggon Fabrik A.G, Panstwowe Zaklady Lotnicze, Philips da Powis Aircraft.
A 1950, wajen ya koma wajen kawo sassan jiragen saman Ma'aikatar Tsaron Turkiyya da gyara su, inda ya fi mayar da hankali ga gyara maimakon kera sababbi
Bayan wannan sauyi, sai Babban Aikin Taimako ya bullo.
Tun da bayan yakin duniya na II Amurka na son mika wa Turkiyya kayan aikin soji ta hanyar taimakon da take bayarwa, sai ayyukan samar da jiragen a cikin gida suka durkushe.
Sannan Amurka ta bukaci da a rushe kamfanin na Jamus da Turkiyya na jiragen sama, bayan yarjejeniyar da aka kulla.
A cikin kankanin lokaci, an samar da jiragen sama 200 a masana'antar tare da taimakon kamfnunnukan kasashen waje.