Wani gungun mutane da ya kunshi magoya bayan kungiyar ta'addanci ta PKK ya kai hari kan masu sanya ido a yayin da ake gudanar da zaben wuri na Turkiyya a Amsterdam, babban birnin Netherlands gabanin wanda za a yi ranar 14 ga watan Mayu.
Gungun mutanen ya kai hari kan masu sanya ido a kan zabe na jam'iyyar People's Alliance a yayin da ake rufe rumfunan zabe a cibiyar RAI Amsterdam Convention Centre ranar Lahadi.
'Yan sandan sun yi gaggawar kai dauki inda suka rika amfani da kulki da karnuna don tarwatsa maharan, wadanda ke rera taken goyon bayan PKK da shugabanta da aka yanke wa hukunci, Abdullah Ocalan.
Sun tsaurara tsaro a yankin har sai da aka kammala zaben, aka kirga kuri'u, aka sanya takardun zaben a buhuna sannan aka ajiye a wuri mai tsaro.
Zaben wuri
An soma zaben wuri ne ranar 27 ga watan Afrilu a shingayen kwastam na Turkiyya da ke kasashen waje. Za a gudanar da zaben a Turkiyya ranar 14 ga watan Mayu.
A zaben shugaban kasa, za a fafata ne tsakanin Shugaba Recep Tayyip Erdogan, wanda ke neman ta-zarce, da Kemal Kilicdaroglu, Muharrem Ince, da Sinan Ogan.
Kazalika jam'iyyu 24 da kuma 'yan takara 151 masu zaman kansu ne ke takarar majalisar dokokin Turkiyya mai kujeru 600.