Jimillar kayan tallafin da aka baiwa Sudan ya kai na dala miliyan 2. / Hoto: AA Archive

Jirgin ruwa dauke da kayan tallafi kimanin tan 2,500 da aka tattara bisa jagorancin Turkiyya da Kuwait, ya isa Sudan wadda yakin da ake yi ke ci gaba da illata ta.

Jami'an gwamnatin Sudan, ciki har da Ministan Watsa Labarai da Raya Al'adu, Graham Abdelkader da Ministan Sufuri Abubakr Abu al Qasim, sun tarbi jirgin ruwan a tashar jiragen ruwa ta Sudan.

Selva Adem, Kwamishinar Ayukan JinƘai a Sudan, ta yada taimakon da Turkiyya da Kuwait ke bayarwa ba gajiyawa.

Ya sake tabbatar da kudirin Sudan na tabbatar da kayan tallafin sun isa ga wadanda suke bukata, inda ya kuma nuna bukatar ci gaba da kai kayan har ma bayan yakin.

Jakadan Turkiyya a Sudan Fatih Yildiz ya ce manufar taimakon ita ce a taimaka wa jama'ar Sudan a ke bukatar tallafi, tare da janyo hankulan uniya ga rikicin jin kan da kasar ke fama da shi.

Ya jaddada cewa a yayinda rikicin Gaza a Falasdin da na Ukraine ke jan hankali, haka ya zama dole da kar a kawar da kai daga rikicin Sudan.

Taimakon da ya kai darajar dala miliyan 2

Mohammed Ibrahim al Hamed, Mataimakin Jakadan Kuwait a Khartoum, ya bayyana cewa taimakon bangarensu ya fito ne daga Kungiyar Jama'ar Tallafi ta Kuwait da ke karkashin Sarki SHaikh Meshal Al Ahmad Al Jaber Al Sabah.

Ya yi tsokaci da cewa taimakon ya kai darajar sama da dala miliyan biyu ind aya tabbatar da cewa Kuwait za ta ci gaba da taimaka wa Sudan a wannan yanayi na tsaka mai wuya da kasar ke ciki.

Sudan na fuskantar rikicin jin kai mafi muni a tarihin baya-bayan nan. Kasar ta fada yakin basasa a watan Afrilun bara a lokacinda sojoji da mayakan RSF suka fara kai wa juna hare-hare.

Tun wannan lokaci, sama da watanni 16 ana fafata yaki tsakanin sojoji d amayakan RSF ina aka kashe sama da mutane 20,000, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar.

TRT World