Isra'ila tana yaɗa farfaganda don ɓata sunan shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ne domin ta yi rufa-rufa kan kisan ƙare-dangin da take yi wa Falasɗinawa da ke Gaza, a cewar Mataimakin Shugaban Jam'iyyar AK kuma kakakin jam'iyyar, Omer Celik.
"Kalaman da ministan harkokin wajen Isra'ila yake yawaita yi kan shugaban ƙasarmu ba komai ba ne face ƙoƙarin yin rufa-rufa game da kisan ƙare-dangi da Isra'ila take yi," in ji Celik a saƙon da ya wallafa a shafin X ranar Asabar.
Ya bayyana haka ne bayan wani saƙo da ministan harkokin wajen Isra'ila, Israel Katz, ya fitar inda ya wallafa hoton Shugaba Erdogan da na shugaban Hamas Ismail Haniyeh suna yin musabaha lokacin da ya kai ziyara Istanbul, yana mai cewa ya kamata shugaban Turkiyya "ya ji kunya".
Katz ya rubuta cewa, "Ƴan Uwa Musulmi: Masu fyaɗe da kisan ƙare-dangi da wulaƙanta gawawwaki da kashe jarirai".
Sai dai Celik ya mayar da martani cewa, "Masu kashe ƙananan yara ba sa son a tsagaita wuta ko kuma duk wata yarjejeniyar zaman lafiya. Waɗannan masu kisan kiyashi ba sa son aiwatar da tsare-tsaren da ke shugabanmu yake jagoranta na tsagaita wuta da zaman lafiya".
"Duk abin da Isra'ila za ta yi, ta sani cewa duniya ta yi Allah wadarai da ita kuma za ta fuskancin hukunci," in ji Celik.