Hukumar MIT tana shirin faɗaɗa ayyukanta game da barazanar leƙen asirin yanar gizo don kare bayanan sirri masu mahimmanci. / Hoto: AA      

Hukumar leƙen Asiri ta Turkiyya (MIT) ta yi nasarar katse shafukan sadarwar wata cibiyar leƙen asiri ta duniya a intanet wadda take tattara bayanan dubban mutane a duniya ciki har da na Turkiyya.

A wani aikin haɗin gwiwa tare da hukumomin cikin gida, MIT ta gudanar da aikin ne a wani ɓangare na binciken da ofishin mai gabatar da ƙara a Ankara babban birnin Turkiyya ya jagoranta, kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana.

Bayanai da aka yaɗa tare ƙungiyoyin ta'addanci

Bayan ɗogon bincike da MIT ta yi, an gano cewa cibiyar leƙen asirin ta yanar gizo wadda ke da alaƙa da ƙasashen duniya, tana musayar bayanan sirri da ta sato da ƙungiyoyi daban-daban, ciki har da na 'yan ta'adda.

Katse shafukan intanet

An kama mutum 11 tare da katse shafuka da dama na intanet da ake zargi da alaƙa da cibiyar leƙen asirin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

MIT na shirin faɗaɗa ayyukanta na yaƙi da barazanar masu leƙen asiri ta intanet don kare bayanan sirri masu muhimmanci da kuma bin diddigin alaƙar kasa da kasa, tare da ƙarfafa ƙuɗurinta na hana ayyukan da ke barazana ga tsaron ƙasar Turkiyya.

TRT World