Kan batun shiga Turkiyya ba bisa ka'ida ba kuwa, jami'in ya ce godiya ga kwararan matakai, don kuwa tun 1 ga watan Janairu aka kama mutum 6,423 da suka hada da 'yan ta'adda 451 da suka kutsa ta kan iyakokin Turkiyya. Hoto: AA Archive

Turkiyya ta "kawar" da fiye da 'yan ta'addan kungiyar YPG/PKK 1,180 tun daga farkon shekarar nan, da suka hada da wadanda ke buya a kan iyakokin arewacin Iraki da arewacin Syria, a cewar Ma'aikatar Tsaron Kasar.

"'Yan ta'adda 39 aka kawar a makon da ya wuce," kamar yadda Ma'aikatar Tsaron Kasar ta shaida wa manema labarai a ranar Alhamis a babban birnin kasar Ankara.

Jami'an Syria sun ce an dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankunan Turkiyya da ke kan iyaka da ake dakile ayyukan ta'addanci da suke taimaka wa wajen magance matsalar.

Tun watan Janairu kungiyar YPG/PKK ta kai hare-hare sau 165 a yankunan da Turkiyya ke yaki da ta'addanci inda aka "kawar" da 'yan ta'adda 864 ta hanyar mayar da martani ba tare da bata lokaci ba da sojojin Turkiyya suka kai.

Barazana ga dan adam

Kungiyar PKK/YPG da yaduwarta na yin barazana ba ga Turkiyya ba kawai, har ma ga al'ummar yankin, a cewar majiyar.

"Abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun hada da na yadda al'ummar yankin ke hada kai don kare 'yancinsu da iyakokinsu daga yadda kungiyar ta'addanci ta YPG/PKK ke kafuwa a wajen. Muna bin diddigin duk abin da ke faruwa."

"Muna sa ran kasashe kawayenmu za su daina bai wa kungiyar ta'addanci ta PKK/YPG tallafi da goyon baya na yakin da muke yi da ta'addanci," majiyar ta jaddada.

A shekara 35 din da ta shafe tana ayyukan ta'addanci ta wajen takalar Turkiyya, Amurka da Turkiyya da Tarayyar Turai sun ayyana kungiyar PKK a matsayin ta ta'addanci - kuma tana da hannu a mutuwar fiye da mutum 40,000 da suka hada da mata da yara da jarirai. YPG ita ce reshen PKK a Syria.

Kan batun shiga Turkiyya ba bisa ka'ida ba kuwa, jami'in ya ce godiya ga kwararan matakai, don kuwa tun 1 ga watan Janairu aka kama mutum 6,423 da suka hada da 'yan ta'adda 451 da suka kutsa ta kan iyakokin Turkiyya.

Kusan mutum 150,584 aka hana su tsallake kan iyakar.

AA