An zabi Darakta Janar na TRT Mehmet Zahid Sobaci a matsayin shugaban kungiyar Asia-Pacific Broadcasting Union (ABU) yayin taronta na 60.
"Zaben da aka yi mini a matsayin shugaban ABU yana da muhimmanci ga manufar Turkiyya ta jagora a kowanne fanni a duniya,” in ji Sobaci, inda ya kara da cewa shugabancin ABU yana da matukar muhimmanci domin kuwa ya zo a lokacin da kasar ta cika shekara 100 da zama Jamhuriya.
Taron ABU, wadda ita ce kungiyar kafafen watsa labara mafi girma a duniya inda fiye da mutum biliyan 3.5 suke kallon kafafen watsa labaran da ke karkashinta kuma take da mambobi 246 daga kasashe 65, an yi shi ne a birnin Seoul daga 31 ga watan Oktoba zuwa 1 ga watan Nuwamba, 2023 karkashin jagorancin Hukumar watsa labarai ta South Korean Broadcasting System.
“Turkiyya tana ci gaba da daukaka da kuma kuma karfi a matsayinta na jagora. Jamhuriyar Turkiyya ta hada kowanne fanni, ciki har da siyasar cikin gida da manufofin kasashen waje da fannin makamashi, muhalli, masana'antu, ilimi da fasaha,” in ji Sobaci.
“Wannan lokaci ne nuna burin Turkiyya, da kuma kwazonta na cim ma abubuwan da ta sanya a gaba. Don haka, muna kallon shugabancin ABU a matsayin wani mataki na taimakawa wajen cim ma muradun Turkiyya a fannin harkokin watsa labarai na duniya," a cewarsa.
'TRT tana shaidu wa duniya abin ke faruwa a duniya'
Sabon zababben shugaban ABU kuma Darakta Janar na TRT ya jaddada muhimmancin tashoshin da kafar watsa labarai nTurkiyya TRT da ke karkashin gwamnatin kasar.
"Da tashoshimu irin su TRT World da TRT Arabic, da kuma sashen labaranmu na dijital na duniya, mun bunkasa zuwa wata cibiyar watsa labarai da ke bayyana abin da ke faruwa a duniya," in ji Sobaci.
“Yayin da muke ci gaba da wannan aiki, ba mu yi watsi da nauyin da ke wuyanmu ba. Mun himmatu wajen gabatar da batutuwan da suka shafi ci-gaba da rikice-rikice da ke faruwa a duniya ta fuskar adalci,” in ji shi.
“Mun himmatu wajen samar da murya ga wadanda ake yawan watsi da su. Dangane da kisan kiyashin da aka yi a Falasdinu, mun himmatu wajen aiwatar da hakan a aikace.”
A yayin jagorancin Sobaci a matsayin shugaban ABU, TRT za ta karbi bakuncin taron kungiyar karo na 61 a Istanbul, wanda ake sa ran za a yi a watan Oktoba na shekarar 2024.