Turkiyya ta "kawar" da ƴan ta'addar YPG/PKK fiye da 1,351 tun farkon wannan shekarar, ciki har da waɗanda suke ɓuya a faɗin kan iyakarta da Iraƙi da arewacin Syria, kamar yadda Ma'aikatar Tsaron Kasar ta bayyana.
"Jumullar ƴan ta'adda 80 aka kawar a makon da ya wuce," kamar yadda wani jami'in Ma'aikatar Tsaron Kasar ya shaida wa manema labarai a Ankara ranar Alhamis.
"Ana ci gaba da ƙoƙarin samar da zaman lafiya ba tare da ɓata lokaci ba a Syira, lamarin da zai ba da damar mayar da ƴan ƙasar yankuna masu aminci lami-lafiya," in ji jami'in, yana mai magana a kan ƙoƙarin Turkiyya na kare faɗaɗar ayyukan ta'addanci a iyakar kasar da Syria da kuma tabbatar da tsaron ƴan Siriyan.
An dauki dukkan matakan da suka dace wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankunan da ake gudanar da samamen, kuma masu kai hare-haren ta'addanci sun gamu da gamonsu, jami'in ya ƙara da cewa.
Tun a watan Janairu ƙungiyar ta'addanci ta YPG/PKK ta kai hare-hare 342 a yankunan da Turkiyya ke yaƙi da ta'addanci, an kuma da "kawar" da ƴan ta'adda 991 ta hanyar martanin gaggawa da sojojin Turkiyya suka kai, a cewar jami'in.
Hukumomin Turkiyya na amfani da kalmar "kawarwa" ne don su nuna cewa ƴan ta'addar da ake magana a kai ko dai sun miƙa wuya ko an kashe su ko kuma an kama su.
Labari mai alaƙa: Jami'an Turkiyya sun 'kawar' da shugaban YPG/PKK a Syria
'Daukan matakan da suka dace'
Da suke amsa wata tambaya da ta shafi rikici tsakanin ƙabilun Larabawa da ƙungiyoyin ta'addanci a arewacin Syria, majiyoyin ma'aikatar tsaro sun ce: "Muna ɗaukar dukkan matakan tabbatar da tsaron dakarunmu da ma'aikatanmu; babu wani abu marar daɗi."
Tun shekarar 2016, Ankara ta ƙaddamar da ayyuka uku na yaƙi da ta'addanci a faɗin iyakarta da arewacin Siriya don daƙile hana kafuwar ta'addanci da kuma samar da zaman lafiya ga mazauna yankin: ayyukan su ne Euphrates Shield (2016) da Olive Branch (2018), da kuma Peace Spring (2019).
A cikin fiye da shekara 35 da ta yi tana aiwatar da ayyukan ta'addanci a kan Turkiyya - ƙungiyar PKK - wacce Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin ta ta'addanci, ta yi sanadin mutuwar mutum fiye da 40,000 da suka haɗa da mata da yara da kuma jarirai. Kungiyar YPG ita ce reshenta a Siriya.
Cibiyar sa ido ta Turkiyya da Rasha da ke Karabakh
Akan tambayar da ta shafi halin da ake ciki yanzu a yankin bayan ayyukan yaƙi da ta'addanci da rundunar sojin Azerbaijan ke yi a Karabakh da kuma ayyukan cibiyar sa ido ta Turkiyya da Rasha kuwa, majiyoyin sun ce suna sa ido sosai akan lamarin.
Cibiyar na ci gaba da ayyukanta kuma ba a gano wata alama ta take yarjejeniyar tsagaita wuta ba a yankin bayan ayyukan da rundunar sojin Azerbaijan ta ƙaddamar, in ji majiyoyin.
A makon da ya wuce ne, bayan da ƙungiyoyin mayaƙan sa kai na Armeniya a Karabakh suka yi wata takalar faɗa, sai Azerbaijan ta ce ta ƙaddamar da "ayyukan yaƙi da ta'addanci" a yankin, don jaddada yarjejeniyar zaman lafiya ta ƙasashe uku da aka cimma a shekarar 2020 tsakaninta da Rasha da Armeniya. Bayan awa 24 ne kuma aka ayyana tsagaita wuta.
Cibiyar, wacce aka samar da ita don sa ido a kan yarjejeniyar ta 2020, tana ci gaba da ayyukanta tun ranar 30 ga waran Janairun 2021.