Fidan ya yi nuni da cewar adawar da ke tsakanin China da Amurka za ta kara tsamari, yana mai nuni ga gogayyar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. / Photo: AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi gargaɗi da cewa dole Turkiyya da ma yankinsu su shirya fuskantar yaƙin da za a iya gwabzawa tsakanin Isra'ila da Iran saboda "akwai yiwuwar hakan ta faru matuƙa".

"Dole ne a kalli yaƙi tsakanin Isra'ila da Iran a matsayin abu da zai iya yiwuwa sosai," in ji Fidan a wata tattaunawa a tashar talabijin a ranar Alhamis.

Ya ƙara da cewa "Na yi amanna cewar wannan lamari zai iya faruwa kuma matakin farko da ƙasashen yankin za su ɗauka shi ne su shirya tunkarar wannan yanayi, a matsayin ƙasa da kuma yanki. Wannan ba abu ne da muke buƙatar ya yaɗu ba. Yaɗuwar yaƙi da tayar da tarzoma a yankin ba su ne abin da muke son gani ko fata ba."

Turkiyya ba ta goyon bayan "duk wani rikici da za a yi da Iran wanda zai rikiɗe ya koma yaƙi," Ankara na adawa da hakan, inda ya yi tsokaci da cewar Tehran na da haƙƙin kare kanta.

Da yake bayani kan manufofin Turkiyya na ƙasashen waje da harkokin tsaro, Fidan ya ce Turkiyya "ba ta sanya idanuwanta a kan ko da taƙi ɗaya na ƙasar wani ba, kuma tana son ƙulla alaƙa ta ci-gaban yankin da zaman lafiya da walwala."

Fidan ya yi nuni da cewar adawar da ke tsakanin China da Amurka za ta ƙara ƙamari, yana mai nuni da gogayyar tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu.

'Buɗaɗɗiyar maƙabarta'

Game da iƙirarin mutuwar shugaban ɓangaren siyasa na Hamas Yahya Sinwar, Fidan ya ce Ankara na jiran tabbatar da hakan daga Hamas, yana mai ƙarawa da cewar babu wani labarin musanta hakan da suka samu.

"Abin takaici Gaza ta zama buɗaɗɗiyar maƙabarta inda ake kashe dubban waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, ana aikata kisan kiyashi," in ji shi.

Ya yi tsokaci da cewar Ankara ta auna ta ga yadda Isra'ila "ta shirya ɗaukar matakin soji na ɗaya bayan ɗaya ta kawar da duk wani da ya fuskance ta, ciki har da Hamas, Hezbollah, Houthi da ke Yemen, da sauransu," ya kuma bayyana fatan Turkiyya na hana yiwuwar buɗe sabon babi na yaƙin.

Da yake bayyana yadda sauran ƙasashen yankin ba sa nuna wa Lebanon irin damuwar da suke nuna wa Falasɗinawa, Fidan ya ce "Akwai dalili a nan. Wannan dalili shi ne, tabbas mai girma da ma'ana. Muna buƙatar kallon dalilan da suka janyo hakan."

TRT World